Cibiyar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA tace zata taimaka da dala miliyan biyu da rabi domin kula da lafiyar iyaye mata da kananan yara
Hukumar UNICEF ta bayyana cewa kusan kananan yara miliyan sha daya a Najeriya suna shan wuya saboda rashin abinci mai inganci.
Wani rahoton da aka yi a yi a jihar New York ya nuna cewa kwana da jarirai a gado daya da iyayensu mata, yakan taimakawa iyayensu mata shayar da su da nono har zuwa lokacin da masanan lafiya suka tsara musu
Kasar Birtaniya zata bada dala biliyan 1.6 ga gidauniyar kudin kasa ta duniya domin yaki da kanjamau, tarin fuka da cutar cizon sauro a cikin shekaru uku masu zuwa da fatar shawo kan cutukan da suke kisa.
Majalisar ta yi gargadin cewa akwai hatsarin sake bullar cutar a wuraren da aka kawar da ita idan ba a gaggauta ja mata burki a wuraren da take yanzu ba
Wakiliyar UNICEF a Najeriya ta ce kasar tana samun nasara a yaki da Polio kuma ta doshi kawar da wannan cuta
Hukumar Lafiya ta duniya (WHO) tace kashi sittin da biyar da digo biyu na masu fama da ciwon shan inna suna sashin arewa maso gabashin Nigeriya.
Kasar Ethiopia ta bada ruhoton samun bullar cutar shan inna guda biyu (WPV-1), wanda ya kawo yawan wadanda aka samu da kwayar cutar a kasar zuwa uku wanda, adadin kuma yana karuwa a yankin na Africa
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, an sam raguwar masu mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kanjamau sakamakon karin magunguna da ake samu.
Masanan kimiyya sun gano wata kwayar sashin jiki wadda suka ce zata iya shawo kan kamuwa da HIV, kwayar dake kawo kanjamau AIDS, daga yaduwa bayan ta shiga cikin jiki.
Bincike ya nuna cewa kimanin mata masu ciki dubu sitiin ne suke mutuwa kowacce shekara domin rashin kulawa.
A kokarinta na kawar da cutar kanjamau, gwamnatin kasar Amurka ta sake bayyana shirinta na hada kai da kungiyoyi da gwamnatoci karkashin shirin shugaban kasa na gaggawa domin kawar da kanjamau
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.