A wani ruhoton da aka buga a jaridar kimiyya, wanda ya bayyana gwajin allurar na farko sun gano cewa daga bincike na farko, allurar bata da wani hadari, kuma tana kawo kariya daga cutar cizon sauro ga masu lafiya.
Yayinda yake maida martani ga wannan ci gaban, shugaban shirin kiyaye cutar cizon sauro, Dr Nnenna Ezeigwe, ya nuna ta a matsayin wani ci gaba da aka samu a wannan fannin ya kuma yabi aikin da ake yi a matakai dabam dabam na sarrafa maganin yaki da zazzabin cizon sauro da zai za a dauki shekara takwas zuwa takwas kafin a gama.
Dr Ezegwei ya bayyana cewa akwai maganin rigakafin da ake kira RTS,S wanda yake mataki na karshe ne na gwaji, kuma idan kome ya tafi daidai za’a fara amfani da shi a 2015. Wannan na cikin matakin gwaji na uku kuma na karshe. Nigeriya na cikin kasashe ukuda ake gwada mataki na karshe. Ana yin gwajin ne a Jos da Enugu.
Dr Ezeigwe yace, idan sakamon gwajin na RTS,S ya ci gaba da nuna alamar nasara, kuma kome ya ci gaba da tafiya kamar yadda aka shirya, zuwa 2015, kungiyar lafiya ta duniya zata bada damar amfani da wannan allurar rigakafin.