Shugaban hukumar lafiya matakin farko na kasa Dr. Ado Mohammad ne ya bayyana wannan jiya a wajen wani taron karawa juna sani da hukumar ta shiryawa ma’aikatan lafiya na kauyuka Makurdi jihar Benue.
Dr. Mohammad yace cutar kanjamau tana ci gaba da zama babbar matsala a Najeriya ya kuma yi gargadin cewa matsaloli da hatsarin da wannan kwayar cutar take kawowa a Nigeriya ta zama babbar damuwa ga ‘yan Nigeriya, hadi da ma’aikatan lafiya, dake kokarin kawar da wannan cuta daga kasar dalili ke nan yace ake kokarin koyarwa da shirye shirye da jihohin kasar gaba daya da nufin rage yaduwar cutar.
Jami’ai sun bayyana cewa, bayan wannan shirin na koyarwar, wanda ake yi a mataki biyar za a kuma tanadarwa ma’aikatan lafiya da isassun kayan aiki don kawar da wannan cutar a sassan jihar Benue.
Sakatariyar jihar Benue mai lura da kungiyar aiwatarwa ta shirin yaki da cutar kanjamau Mrs. Ashi Wende ta gargadi mahalrta taron suyi amfani da abinda suka koya wajen kawar da wannan muguwar kwayar cutar a jihar.