A wani gagarumin ci gaba, an zabi Bola Ahmed Tinubu, shugaban Najeriya a matsayin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.
Kusan mako guda kenan da aka kwashe ana cece-kuce tsakanin yan Kamaru kan gina wani katafaren gidan aiki na shugaban hukumar tattalin arziki da zamantakewar kasa, Ayang Luc da ya kai CFA biliyan biyu.
Babban jami'in tsaro na ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya Brigediya Janar MATT MUNRO, ke bayyana haka yayin ziyara a hedkwatar rundunar ta MNJTF a birnin N''djamena dake kasar Tchadi.
A jamhuriyar Nijer mako 1 bayan bayyanar sakamakon jarabawar daliban da ke neman takardar shaidar kammala karatun share fagen shiga jami’a, gwamnatin kasar ta yanke shawarar bai wa wani rukunin dalibai damar sake rubuta gwajin lissafi sakamakon wasu kura-kuran da aka gano a gwajin.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya jagoranci bikin kaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki da hasken rana a birnin Yamai a ci gaba da neman hanyoyin warware dadadiyar matsalar wutar da ake fama da ita a kasar da ke sayen wani bangaren wutar lantarki daga kamfanonin Najeriya.
Masu sharhi akan sha’anin tsaro sun hango cewa kungiyoyin ta’addancin Arewacin Mali sun fara yunkurin kafa reshe a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda bayanai ke nunin yadda suke sajewa da jama’a su na ratsa wasu jihohin Jamhuriyar Nijar don shiga Najeriya cikin ruwan sanyi.
A cikin kwanaki hudun da suka gabata, 'yan sanda a birnin Sfax da ke kudancin Tunisiya sun yi ta aikata zalunci, suna bugu da yin lalata da 'yan ci-rani da masu neman mafaka daga yammacin Afirka, kafin daga bisani su fatattake su zuwa Libya.
Shugaban Kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya kaddamar da gidan tarihi domin karrama tsohon shugaban kasar Ghana marigayi Dr. Kwame Nkruma bisa irin mahimiyar rawar da ya taka wajen ci gaban kasar.
‘Yan bindiga a Nijar na cigaba da amsa kiran hukumomi kasar ta hanyar ajiye makamanai inda suke fitowa suna rungumar shirin zaman lafiya.
‘Yan kasar Senegal mazauna jamhuriyar Nijer sun bayyana farin ciki bayan da shugaba Macky Sall ya sanar cewa ba zai yi tazarce ba a zaben da za a yi a watan fabrerun 2024 koda yake a cewarsu lamarin na bukatar taka-tsan-tsan.
Matsalar wutar lantarki a jamhuriyar Nijer ta haifar da damuwa a wajen al’umma sakamakon lura da yadda a ‘yan kwanakin nan a ke fuskantar daukewar wuta akai-akai inda a kowace rana akan shafe lokaci mai tsawo ba tare da an sami wutar ba lamarin da ke shafar al’amuran rayuwar yau da kullum.
Domin Kari