Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: Cece-Kuce Game Da Ginawa Babban Jami'in Gwamnati Gidan CFA Biliyan Biyu


Luc Ayang - shugaban hukumar tattalin arziki da zamantakewar kasar Kamaru
Luc Ayang - shugaban hukumar tattalin arziki da zamantakewar kasar Kamaru

Kusan mako guda kenan da aka kwashe ana cece-kuce tsakanin yan Kamaru kan gina wani katafaren gidan aiki na shugaban hukumar tattalin arziki da zamantakewar kasa, Ayang Luc da ya kai CFA biliyan biyu.

Ayang Luc wanda ya kwashe shekaru 39 yana yiwa shugaban kasa aiki na bukatar gida da zai ci biliyan biyu na CFA Kamaru, bai tsaya a nan ba ya kuma bukaci ya mallaki motar aiki mai tsadar miliyan da 120 na CFA.

Wannan al'amarin ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan Kamaru da dama, bangaren gwamnati dana 'yan adawa zuwa fararen hula da shafukan sada zumunta, wadanda suke ganin cewa fitar da makudan kudade domin gina wa ma’aikacin gwamnati gidan biliyan 2 har da motar hawa mai tsadar miliyan 120 bai dace ba.

Duba ga yadda kasar ke dauke da dimbin bashi akanta. Tana kashe kudade ta hanyar da bai dace ba, da matsalolin dake gabanta kamar rashin ingantattun ababen more rayuwa, musamman a wasu yankunan kasar.

Philippe Nanga shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam mai taken « Un Monde Avenir » a Kamaru kan wannan matsalar ya ce :

Kun san irin wahala da mutane ke sha musamman a birnin Douala a damuna kamar yanwu. Ya gwamnati za ta bar gyaran hanya domin ta gina gidan zaman mutun da kusasn biliyan 2 na CFA

Charles Njikam dan jam’iyar adawar MRC shi kuma yace

Wannan rainin hakali ne. Ku yan jarida kafin ku karaso nan anguwa na kun ga irin wahala da kuka sha saboda mummunar hanya. Baya da haka, ga matsalar ruwan sha da wutan lantarki, ballantana samun kudin sayan magunguna yayin da ake fama da rashin lafiya. A gaskiya wannan rainin hankali ne.”

Ayang Luc ya samu goyon baya daga jam'iyya mai mulki RDPC. Jean Claude Youth na daya daga cikin ma goya bayan wannan ra’ayi. Ya ce wa manema labarai

Shugaban hukumar tattalin arziki da zamantakewa kamar sauran manyan jami'an gwamnati nada damar mallakar gida na aiki. Yin haka bai saba wa shari’a ba. Saboda haka sai mun ga an fara wannan aiki sannan mu tabbatar da wannan labari. Baya da haka, kadan kun duba wannan takarda da aka yada a yanan gizo, babu tambarin wanda ya bada wannan kwangilar. Don haka sai ayi la’akari da gaske.”

Ba karon farko bane da yan siyasa da kugiyoyin fararen hula ke kalubalantar yadda gwamnati take kashe makudan kudade ta hanyoyin da basu dace ba. Ita kanta gwamnatin kasar ta bakin firaminista na neman rage kudaden da take kashewa wajen daukar dawainiyar ministocinta da sauran jami'anta.

Ga kuma kudaden da Kamaru ke kashewa na matsalar tsaro a arewa mai nisa da arewa maso yamma da kuma kudu maso yammaci.

Ayang Luc ya kasance matsayi na biyar bayan shugaban kasa Paul Biya kuma shine daya daga cikin wadanda suka fi jimawa kan madafun iko a mulkin Paul Biya tun 1983.

Saurari rahoton Mohamed Ladan a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG