Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fafutuka Na Kokarin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Arewacin Kasar Nijar


Taron hanyoyin warware matsalolin tsaro
Taron hanyoyin warware matsalolin tsaro

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin al’umma na kokarin kawo karshen tashe tashen hankula a yankin arewacin kasar, inda jami’ai da masu rajin kare hakkin bil’adama da kungiyoyi masu zaman kansu suka tattauna kan samun hanyoyin magance matsalolin tsaro.

Manufar kungiyoyin ita ce shirya irin wadannan taruruka a wani yunkuri na diba irin rawar da za su takawa domin zakulo hanyoyin warware matsalolin tsaro da suka addabi al’umma a arewacin kasar.

Abubakar Dawa, wani dan kungiyar farar hula a Agadas ya ce suna fatan gwamnati za ta nemi hanyoyi da za ta kare al'umma.

Kungiyoyin sun bukaci ga gwamnatin Nijar da ya kara azama wajen dakile sabuwar matsalar tsaron dake fuskanta tareda kawo karshen zaman kashe wando a tsakanin al’umma, inji Sidi Mamadu wani dan fafutuka a Agadas.

Kungiyoyi daban-daban ne de suka halarci taron inda suka bayyana cewa sha’anin tsaro magana ce da ta shafi dukkan yan kasa.

Kungiyoyin sun rubuta matsalolin tsaro, da arewacin Nijar ke fuskanta inda zasu mikawa hukumomi domin daukar matakkan kawo karshen matsalolin.

Saurari rahoton Hamid Mahmud a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

XS
SM
MD
LG