A baya-bayan nan ne kungiyar ECOWAS ta yi taro a Abuja a cikin watan Agusta inda ta sanya wa'adin kwanaki 7 ga gwamnatin mulkin sojan Nijar don maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, ko kuma ta fuskanci mummunan sakamako, wanda zai iya hadawa har da karfin soji.
‘Yan Najeriya mazauna Nijar sun yi taro da nufin gamsar da ‘yan kasar ta Nijar tasirin kasar, da ma karfin huldar da ke tsakanin kasashen, su na masu bayyana cewa ba da sunansu kungiyar CEDEAO ta bai wa sojojin Nijar wa'adi ba.
‘Yan Najeriya mazauna yankunan da ke daura da iyakokin Jamhuriyar Nijar na ci gaba da zaman rashin tabbas kan abin da ka iya biyo bayan wa'adin da kungiyar ECOWAS ta bayar ga gwamnatin mulkin soji da suka hambarar da gwamnatin farar hula a kasar.
Wata hira ta musamman da wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Nijar game da rashin Zartas da kudurin CEDEAO.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata muhimmiyar ganawa da gwamnonin jihohin Najeriya dake da iyaka da kasar Jamhuriyar Nijar.
A yayinda wa’adin da ECOWAS ta bayar don mayar da shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan mukaminsa ya shude a jiya Lahadi, sojojin da suka yi juyin mulki sun kara tsaurara matakai da nufin tunkarar barazanar amfani da karfin sojan da kungiyar ECOWAS ta ayyana don korarsu daga fadar ta shugabancin Nijar.
Gwamnatin mulkin sojan ta Nijar, ta sallami wasu jakadun kasar da suka hada da na Amurka, Faransa, Najeriya da Togo.
Farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi a birnin Agadas da ke arewacin Nijar kwanaki kalilan bayan da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta kakaba takunkumin karya tattalin arziki ga kasar.
Jagoran sojojin da suka yi juyin mulki ya yi wannan ikirarin ne a wani lokacin da ake jiran zuwan tawagar ECOWAS/CEDEAO karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar domin samo bakin zaren wannan rikici cikin ruwan sanyi.
Manazarta sha’anin tsaro na ci gaba da bayyana matsayinsu dangane da barazanar amfani da karfi da kungiyar CEDEAO ta yi wa sojojin Nijer akan bukatar su mayar da hambararen shugaba Mohamed Bazoum kafin cikar wa’adin mako daya.
Bayan kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma (ECOWAS) ta kakaba takunkumi ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Nijar, wasu mashaharta a kasar Ghana sun bayyana ra’ayinsu game da matakin da ECOWAS ta dauka kan kasar Nijar.
Shugabannin soji na kungiyar ECOWAS na yammacin Afirka sun tattaunawa a Najeriya jiya Laraba game da juyin mulkin da aka yi a Nijar a makon jiya.
Domin Kari