Mashahartan suka ce matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan sojojin da suka yi juyin mulkin ya yi daidai, domin hakan zai zama izna ga wasu da ke da burin yin juyin mulki a nan gaba. Rashin daukar tsattsauran matakin kan kasashen Mali, Burkina Faso da Guinea da suka yi juyin mulki a baya baya nan ya taimaka wajen wannan juyin mulkin, in ji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Yunus Swalahudeen Wakpenjo.
Baya ga takunkumin ECOWAS, kasar Faransa da ta yi wa Nijar mulkin mallaka, ta yi Allah wadai da juyin mulkin. Kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da hadin gwiwar tsaro da taimakon kudi ga Nijar, yayin da Amurka ta yi gargadin cewa taimakon da take bayarwa ga kasar na cikin hadari.
Saurari rahoton Idris Abdullah a sauti:
Dandalin Mu Tattauna