Da suke maida martani kan ikirarin na ECOWAS , kasashen Mali da Burkina Faso sun lashi takobin kai dauki wa sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijer muddin kungiyar ta kasashen yammacin Afrika ta yi amfani da karfin soja wajen warware wannan rikici.
To sai dai kamar yadda za a ji a tantaunawarsu da wakilin muryar Amurka, Souley Moumouni Barma, mai sharhi kan sha’anin tsaro Dr Seidik Abba na ganin Mali da Burkina Faso ba su da karfin da zai ba su damar taka wata babbar rawa idan aka yi katari CEDEAO ta zartar da kudirinta kan sojojin na Nijer.
Saurari hirarsu a sauti:
Dandalin Mu Tattauna