Kamar yadda ya zama al’ada tun bayan juyin mulkin da suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum, majalisar sojoji ta CNSP ta hanyar kakakinta Colonel Major Amadu Abdourahamane da ya bayyana a kafar talbijan mallakar gwamnati ta sanar da jama’ar Nijer wasu matakan da ta dauka don murkushe hare haren sojan da kungiyar CEDEAO ta kudiri aniyar kai masu dazaran sun yi fatali da umurnin mayar da hambararren shugaban akan mukaminsa.
Ya ce duk da yadda al’ummar Nijer da na kasashen CEDEAO suka nuna rashin amince wa da matakin sojan da ake hasashen amfani da shi, bayanai na nunin an jibge dakarun wannan yaki a wasu kasashe 2 na tsakiyar Afrika.
"Majalisar CNSP na bin diddigin tasre tsaren wannan yaki da ake shirin kaddamarwa da izinin CEDEAO, saboda duniya ta sani duk kasar da ta bada damar kai wa Nijer farmaki to za mu dauketa tamkar abokiyar gaba."
Wadanan sojoji da ke zargin CEDEAO da zama ‘yar amshin shatan wata babbar kasa sun ce suna da bayanai dake tabbatar da cewa shirye shiryen kai wa Nijer hari daga wata makwafciyar kasa sun kankama saboda haka majalisar CNSP ta yanke shawarar rufe sararin samaniyar kasar ga kananan jirage daga jiya Lahadi 6 ga watan Agusta sai yadda hali ya yi. Sanarwar ta kara da cewa sojojin Nijer za su maida kakkausan martani ga duk wani yunkurin ratsa sararin samaniyar kasar.
A yayinda ake kyautata zaton yiyuwar fuskantar hare haren soja sakamakon shudewar wa’adin kungiyar ECOWAS bayan gangamin da suka yi a filin kwallon kafa na Stade Kountche, gungu gungun matasa sun tattaru a wurare daban daban na gundumomin 5 na birnin Yamai a cikin dare jiya domin yin abinda suka kira kare kasa daga katsalandan din kasashen waje.
Tun a yammacin ranar Asabar labarin wani ayarin sojan Faransa da aka hango a garin Ouaillam kan hanyar su ta zuwa Yamai ya karade kafafen sada zumunta wanda wasu suka dauka a matsayin shirin afakawa sojan CNSP to amma ofishin jakadancin faransar a sanarawr da ya fitar ya karyatar da wadanan bayanai. Yana mai cewa dakarun da ake magana a kansu sun shafe watanni suna aiyukan sintiri na hadin gwiwa da takwaorinsu na Nijer don yaki da ta’addanci .
Koda yake jama’a na gudanar da harkoki ba tare da wata damuwa ba hankulan mazauna birnin Yamai sun karkata a tsawon daren jiya wajen fadar shugaban kasa don jin yadda za ta kaya sakamakon barazanar da kungiyar ECOWAS ta yi wa Janar Abdourahamane Tchiani da mukarrabansa.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna