Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankali Ya Tashi A Yankin Sahel Yayin Da Makwabta Ke Gargadi Kan Tsoma Bakin Juyin Mulkin Nijar


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Shugabannin soji na kungiyar ECOWAS na yammacin Afirka sun tattaunawa a Najeriya jiya Laraba game da juyin mulkin da aka yi a Nijar a makon jiya.

A farkon makon nan ne kungiyar tattalin arzikin yankin ta sanya wa'adin maido da mulkin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, ko kuma ta fuskanci yiwuwar shiga tsakani na soji.

Gargadin ya haifar da kakkausar suka daga wasu makwabtan Nijar guda biyu wadanda kuma suke da shugabannin da suka hau karagar mulki ta hanyar juyin mulki.

Shugaban Niger Mohamed Bazoum
Shugaban Niger Mohamed Bazoum

Yayin da ya rage kwanaki hudu wa’adin mayar da mulki ga zababben shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya cika, da kuma makwabciyar Nijar Mali da Burkina Faso suke gargadi kan duk wani shiga tsakani na soji, tashin hankalin ya kara ta’azzara a yankin Sahel a wannan makon.

Nassirou Seydou shi ne shugaban kungiyar rajin kare hakkin dan Adam ta “Voice of the Voiceless. Da yake magana da Muryar Amurka daga Yamai babban birnin Nijar, ya ce baya tsammani Kungiyar ECOWAS za ta shiga tsakani ta hanyar soji domin ba ta yi a Burkina Faso ko Mali a lokacin juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan ba.

Ya ce kamata ya yi tattaunawa ta zama babban mataki a irin wadannan yanayi.

Sai dai idan aka yi la’akari da takun-saka da abokan huldar Nijar na yanzu kamar Faransa da Amurka, Seydou ya ce, sabbin shugabannin sojan na iya komawa ga wasu kasashe don neman taimako a yankin.

Antony Blinken
Antony Blinken

A yayin da ake ta takun saka tsakanin Nijar da Faransa, tsakanin sojoji da fadar shugaban kasar Faransa, lamarin bai dace da a ci gaba da dangantaka ba, “musamman ma idan ana maganar Faransa da kawayenta na taimakawa Nijar wajen fita daga cikin halin da ake ciki. Don haka ya sa sojan Nijar ba shi da wani zabi illa duba wani waje.”

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya yi magana da shugaban Nijar Bazoum da yammacin jiya Talata, ya kuma jaddada goyon bayan Amurka da kawayenta na gudanar da mulkin dimokradiyya.

“Gaskiya lamarin shine cewa Tchiani, jagoran juyin mulkin, yana jefa duk wannan cikin hadari. Ya sanya duk taimakon Amurka cikin haɗari. Ya riga ya rasa tallafin kasafin kudin Faransa. Faransawa sun yanke tallafin da suke bayarwa, Amurka na iya yanke taimakon da take bayarwa, watakila Amurka za ta katse taimakon tsaro."

Yayin da wasu ke cewa martanin da kasashen duniya suka mayar kan juyin mulkin ya dace sosai, Shurkin ya ce katse tallafin na iya haifar da wasu sakamakon.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG