Adadin na daf da karuwa zuwa mutane miliyan 52.7 nan da tsakiyar shekarar 2025, ciki har da mutane miliyan 3.4 dake fama da matsananciyar yunwa a cewar WFP
Yayin da aka yankewa Adegboruwa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan kaso, aka yankewa Isong hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 10.
Kudirin ya yi tanadin daurin shekaru 3 ga wanda aka samu da laifin aikata luwadi ko madigo da kuma daurin shekaru 5 ga wanda aka samu da laifin daukar nauyin ayyukan ‘yan luwadi da madigo.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuryar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi jawabi ga al’umma ranar bukin samun 'yancin kai inda ya tabo mahimman batutuwan da suka shafi tafiyar kasar daga lokacin da ya kwaci madafun iko zuwa yau.
A baya kungiyar ECOWAS mai mambobi 15 ta yi shirin kaddamar da kudinta a shekarar 2020, sai dai barkewar annobar Korona ya haifar da tsaiko.
Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan da ya zura kwallaye 3 a wasan karshe na gasar Europa wacce kulob din nasa ya lashe.
'Yan Nijer, sun yi tsokaci game da amincewa da ficewa daga Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka da Mali, Burkina Faso, da Nijer su ka yi.
A karon farko cikin kusan shekaru 50 na wanzuwar kungiyar mai mambobin kasashe 15, gwamnatin soji ta Nijar, Mali, da Burkina Faso sun sanar a watan Janairu cewa sun yanke shawarar ficewa daga ECOWAS.
Daga cikin wadanda suka halarci taron a babban birnin Najeriya, Abuja, har da Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, wanda aka nada a matsayin mai shiga tsakani da kasashen da suka balle daga ECOWAS a watan Yuli, daga cikin ƙasashe 15 da ke cikin kungiyar.
Kasashen AES sun bada sanarwar yanke shawarar bai wa al'umomin kasashen ECOWAS ko CEDEAO izinin kai-komo a yankin AES Sahel ba tare da bukatar takardar bisa ba. Abin da ke zama wani matakin riga kafi, a dai dai lokacin da kasashen ECOWAS ke taro yau a Abuja kan batun ficewar su daga kungiyar.
Zafafar wannan fadan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi, da na Rwanda Paul Kagame za su gana a yau Lahadi a kasar Angola, wadda ke shiga tsakani a rikicin.
A yayin da ECOWAS ke Shirin gudanar da taro a ranar lahadi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya domin tantauna makomar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wadanda wa'adin ficewar su da ga kungiyar ke cika a watan janairun shekarar 2025, kasashen sun ce bakin alkalami ya riga ya bushe.
Domin Kari
No media source currently available