Harin ta sama ya faru a kasuwar mako-mako ta garin, inda mazauna yankin daga kauyukan dake makwabtaka suka taru domin saye da sayarwa.
Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Nijar CODDH ta yi wa hukumomin mulkin sojan kasar hannunka mai sanda dangane da batun mutunta yarjeniyoyin kasa da kasa kamar yadda suka yi alkawari bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin bara, yayin da ake bikin ranar kare hakkin 'dan adam ta duniya ,
Kungiyoyin sun yabawa Ghana da ‘yan kasar bisa gudanar da zaben Shugaban kasa da na Majalisun dokoki cikin lumana.
Mr John Dramani Mahama ya samu kuru’u miliyan 6,328,397, wanda ya yi dai dai da kashi 56.55 cikin dari. Yayin da Bawumia na NPP ya samu kuru’u miliyan 4.657.304, wanda ya yi dai dai da kashi 41.67 cikin dari
A yayinda ake bikin tunawa da ranar yaki da cin hanci ta duniya a yau 9 ga watan Disamba kungiyar Transparency International reshen Nijar ta bayyana damuwa game da abin da ta kira tarnakin da ake fuskanta a wannan gwagwarmaya sakamakon wasu dalilan da ke da nasaba da raunin doka
Wasu manyan jami’an hukumar Majalisar Dinkin Duniya sun kammala ziyarar kwanaki da suka kai a Nijar, don tattauna batutuwan tsaro, yanayin bakin haure da ‘yan gudun hijira a jihar Agadez
A Ranar Lahadi dantakarar jam’iyar New Patriotic Party mai mulki a Ghana, mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasar.
Bawumia ya kuma taya abokin hamayyarrsa John Dramani Mahama murnar nasarar lashe zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disamban 2024.
Ouedraogo ya yi aiki a majalisar ministocin firaminista mai barin gado, Apollinaire Joachim Kelem de Tambela, wanda Kyaftin Ibrahim Traore ya cire daga mukaminsa a ranar Juma'a.
An riga an kai gawar mamacin dakin ajiyar gawarwaki domin adana da bincike, yayin da wanda ya jikkata ke samun kulawar likitoci.
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.
Zababben Shugaban Amurka Dobald Trump ya wallafa wasu sakonni a kafafen sada zumunta na barazanar kara haraji kan Canada, China da Mexico
A jihar Kano dake Najeriya ana zargin wani da cin zarafin wata ma'aikaciyar jinya mai dauke da juna biyu a asibitin yara ta Isyaka Rabiu
A Nijar an bude wata kasuwar baje koli ta ayyukan hannu da ake kira SAFEM, da matan kasar ke halarta daga jihohin da wasu kasashen Afirca