Shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ta ECOWAS sun gudanar da taro ranar Lahadi, inda tsaro da ficewar kasashen uku da ke karkashin mulkin soji suka kasance a kan gaba a ajandar taron.
Gabanin taron kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun sake jaddada cewa matakinsu na ficewa daga kungiyar ya zama "wanda ba za a iya sauya ba," suna kuma sukar kungiyar da zargin zama ‘yar amshin shatar Faransa da ta mallake su.
Ficewar wadannan kasashe uku na iya yin tasiri mai girma kan cinikayya da zirga-zirgar mutane ba atre da wani shinge ko biyan kudi ba, da kuma haɗin kai kan harkokin tsaro a yankin da ƙungiyoyin jihadi ke ci gaba da samun ƙarfi a fadin yankin Sahel.
Daga cikin wadanda suka halarci taron a babban birnin Najeriya, Abuja, har da Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, wanda aka nada a matsayin mai shiga tsakani da kasashen da suka balle daga ECOWAS a watan Yuli, daga cikin ƙasashe 15 da ke cikin kungiyar.
Dandalin Mu Tattauna