A yayin da ECOWAS ke Shirin gudanar da taro a ranar lahadi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya domin tantauna makomar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wadanda wa'adin ficewar su da ga kungiyar ke cika a watan janairun shekarar 2025, kasashen sun ce bakin alkalami ya riga ya bushe.
Tan 60,000 na tataccen man fetur din da matatar ta fara fitarwa ketare zai isa ga kamfanin Neptune Oil, daya daga cikin manyan dillalan albarkatun man fetur a yankin tsakiyar Afirka.
Wata sanarwa da gwamnatin Nijar ta fitar ce ta bayyana hakan a ranar Laraba
Shugaban hukumar kula da kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana damuwa game da cewar a daidai lokacin da kungiyar ke shirye-shiryen fara shagulgulan bikin cikarta shekaru 50 da kafuwa, mambobinta guda 3 sun bayyana aniyarsu ta ficewa daga cikinta.
Harin ta sama ya faru a kasuwar mako-mako ta garin, inda mazauna yankin daga kauyukan dake makwabtaka suka taru domin saye da sayarwa.
Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Nijar CODDH ta yi wa hukumomin mulkin sojan kasar hannunka mai sanda dangane da batun mutunta yarjeniyoyin kasa da kasa kamar yadda suka yi alkawari bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin bara, yayin da ake bikin ranar kare hakkin 'dan adam ta duniya ,
Kungiyoyin sun yabawa Ghana da ‘yan kasar bisa gudanar da zaben Shugaban kasa da na Majalisun dokoki cikin lumana.
Mr John Dramani Mahama ya samu kuru’u miliyan 6,328,397, wanda ya yi dai dai da kashi 56.55 cikin dari. Yayin da Bawumia na NPP ya samu kuru’u miliyan 4.657.304, wanda ya yi dai dai da kashi 41.67 cikin dari
A yayinda ake bikin tunawa da ranar yaki da cin hanci ta duniya a yau 9 ga watan Disamba kungiyar Transparency International reshen Nijar ta bayyana damuwa game da abin da ta kira tarnakin da ake fuskanta a wannan gwagwarmaya sakamakon wasu dalilan da ke da nasaba da raunin doka
Wasu manyan jami’an hukumar Majalisar Dinkin Duniya sun kammala ziyarar kwanaki da suka kai a Nijar, don tattauna batutuwan tsaro, yanayin bakin haure da ‘yan gudun hijira a jihar Agadez
A Ranar Lahadi dantakarar jam’iyar New Patriotic Party mai mulki a Ghana, mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasar.
Domin Kari
No media source currently available