Gwamnatin Kamaru ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa shugaba Paul Biya ya rasu.
Samar da tsabtataccen ruwan sha ga al’umma nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati saidai a kasashe masu tasowa irin su Nijar kaso mai yawa na al’aumma ne baya samun ruwa wanda ke zaman ginshikin rayuwa
Shugaban mai shekaru 66 da haihuwa ya fada a cikin wani jawabi a hedkwatar yakin neman zaben sa cewa, “Za mu tsarkake kasar daga dukkan masu cin hanci da rashawa da kuma mazambata.”
Shawarar ta hada da maganar aika karin sojoji a yankin hade da bukatar shigar da matasan yankin a ayyukan yaki da ta’addanci.
Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, a karon farko ya mayar da martani kan sukar da ake masa dangane da zargin hannu a kamawa da kuma daure wasu masu fafutukar yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da aka fi sani da ‘Galamsey’ a Ghana.
An gudanar da bikin Ranar Malaman Makaranta ta Duniya ta bana - 2024, wanda majalisar dinkin duniya ta ware a shekarar 1994 da nufin karfafa wa malamai guiwa a ayyukan ilmantar da al’umma.
Harin an kai shi ne a kan dakarun sa kai na RSF, a wani mataki na farmakin soja mafi girma tun bayan barkewar rikicin.
A yayinda aka fara girbe amfanin gona a yankuna da dama na jamhriyar Nijar ofishin ministan kasuwanci ya hana fitar da abincin da suka hada da shinkafa da hatsi da dawa zuwa ketare da nufin samar da wadatar cimaka akan farashi mai rangwame a kasuwannin kasar.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana damuwarsa ga hafsan hafsoshin sojin Sudan a game da yadda ricikin kasar yake dada ruruwa, yayin da suka gana a wani taron manyan jakadu a birnin New York a ranar Laraba.
Lauyansa ya ce lafiyar al-Bashir tana tabarbare wa a baya bayan nan, yana mai cewa amma yanayin bai tsananta ba.
Hukumomim Burkina Faso sun ce sun yi nasarar dakile wasu hare-haren ta’addancin da aka yi yunkurin kai wa a lokaci guda a wasu mahimman wuraren birnin Ouagadougou ciki har da fadar shugaban kasa.
Domin Kari
No media source currently available