A wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta France 24 a baya-bayan nan, shugaban ya yi watsi da ikirarin cewa, kamen na da alaka da siyasa ko kuma nufin dakile zanga-zanga.
Shugaban Akufo-Addo ya shaida wa gidan talabijin na France 24 cewa: “Ba ni da hurumin daure mutane a Ghana, kotuna a Ghana hukumomi ne masu zaman kansu, kuma haka suke tun tsawon wannan lokaci na jamhuriya ta hudu. Mutanen sun yi rashin da’a kuma an gurfanar da su a gaban kotu, kotu ce ta daure su. Babu batun siyasa ko sa bakin bangaren zartarwa. Halayyarsu ita ce ta sanya su cikin matsala da 'yan sanda da kuma kotuna”.
Antoni janar kuma ministan shari’a, Godfred Yeboah Dame ne ya shigar da karar masu zanga-zanga 53 da aka kama a yayin da ake gudanar da zanga-zanga na kwanaki uku da wani gungun matasa ya shirya daga ranar 3 zuwa 5 ga watar Oktoba 2024, domin matsin lamba ga gwamnati da ta yaki barnar muhalli da illa ga albarkatun kasa da suka hada da koguna da gandun daji, da Galamsey ya haifar.
Masana da kwararrun lauyoyi sun amince da ikirarin shugaba Akufo-Addo cewa ba shi da hurumin kama su, sai dai sun yi Allah wadai da rike masu zanga-zangar har fiye da awanni 48 ba tare da ba da belinsu.
Lauya Anas Mohammed ya shaida wa Muryar Amurke cewa: “Dokar Ghana ba ta yarda da a kama dan zanga-zanga ko wani fiye da awa 48 ba’a kais hi kotu ba.
A na sa bangaren, Yunus Salahudeen Wakpenjo, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya ce da ya kamata shugaban kasa ya yi la’kari da cewa manufar zanga-zangar na da kyau, domin haka da sai ya yi musu afuwa a sake su. Ya kara da kira ga shugaban kasa da ya ba da umarnin a sake su, su koma ga iyalansu.
Sai dai, jami’in sadarwa na jam’iyar NPP mai mulki, Alhaji Ali Kabe, ya amince da matsayin shugaban kasa, domin: A matsayinsa (shugaban kasa) na lauya, ya san lokacin da ya kai, don yin afuwa ga wani; shin wadannan (‘yan zanga-zanga) sun cancanci a yi musu afuwa? … sai in ce (lokaci) bai kai ba. Dalilin da ya sa ya yanke maganar ke nan, ya ce shi ba zai hana zanga-zaga ba, kuma ba zai sa baki a harkar kotu ba”.
Wannan kalamai na shugaba Akufo-Addo ya zo a daidai lokacin da muhawarar da ta shafi Galamsey ke kara ta’azzara, inda al’ummar yankin ke fama da gurbatattun koguna da sare itatuwa saboda ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ke kokawa.
Yunkurin da gwamnati ke yi na murkushe Galamsey na fuskantar kalubale, ciki har da zargin cin hanci da rashawa da rashin aiwatar da dokoki.
Masu zanga-zanga kuma na ganin gwamnati ba ta yi abin da ya dace wajen tunkarar lamarin ba, yayin da gwamnati ke ganin cewa yaki da Galamsey na bukatar sa hannun kowa da kowa, da kuma bin doka da oda.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdalla Bako:
Dandalin Mu Tattauna