Taron kwamitin shugabannin al’umomin karkarar Bankilare ta jihar Tilabery ya shawarci hukumomin jamhuriyar Nijar a game da bukatar daukan wasu matakan da suke ganin zasu taimaka a warware matsalolin tsaron da suka addabi yankin iyakokin kasashe 3.
Shawarar ta hada da maganar aika karin sojoji a yankin hade da bukatar shigar da matasan yankin a ayyukan yaki da ta’addanci da dai sauransu.
Tsanantar al’amuran tsaro a yankin da ake kira yankin iyaka 3 wato wurin da Nijar da Mali da Burkina Faso ke makwabtaka matsala ce da kai tsaye ke shafar karamar hukumar Bakilaren jihar Tilabery.
Sakamakon yadda abin ke dabaibaiye tafiyar harakokin jama’a na yau da kullum dalili ke nan bayan nazarin halin da ake ciki shugabanin al’umomin da abin ya shafa a karshen taron da suka gudanar a Yamai suka bullo da wasu shawarwarin da suke fatan ganin shugaban gwamantin mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani da mukarabbansa na CNSP sun dauke su da mahimmanci.
Labgata Sidi Saghid shi ne kakakin wadanan shugabanni, ya ce ‘’Mu mutane Bankilare muna kira ga CNSP ta dauki matakai don kare manoman da suka yi aiki a damanr bana da amfanin gonan da suka samu, sannan muna bukatar a bude makarantun da suka shafe shekaru da dama a rufe. Asibitin da aka gina tun 2016 bai taba aiki ba, muna fatan za a budeta daga yanzu.’’
Ya ce ‘’Muna kiran CNSP ta dauki matakai don mayar da dukkan ‘yan gudun hijirar cikin gida zuwa garuruwansu na asali a kuma tura karin jami’an tsaron da zasu basu kariya su da dukiyoyinsu.
Ya kara da cewa, “Muna fatan za’a karfafa ayyukan sinitiri a kowane lungu da sako na kananan hukumomin Bankilare, Kokorou, Gorouol da Tera tare da fatan ganin hukumomin CNSP sun shigar jama’ar wadanan kananan hukumomi a ayyukan yaki da ta’addanci ta hanyar bai wa matasan karkarar damar shiga aikin tsaron kasa.
To ko me masu sharhi ke cewa kan tasirin wadanan shawarwari na al’umomin karkarar Bankilare? Abass Moumouni, kwararre ne kan sha’anin tsaro, ya ce tabbas ana iya sa ‘yan Bankilare cikin harkar tsaro a horar da su kuma a kai su wasu wurare.
Kamar yadda abin yake a Mali da Burkina Faso, lalacewar al’amuran tsaro na daga cikin dalilan da sojojin Nijar suka ayyana a jerin hujjojin kifar da gwamnatin farar hula a watan Yulin shekarar 2023.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna