Kungiyar ‘yan tawayen sudan ta RSF da kawayenta sun aikata munanan laifuffukan cin zarafi ta hanyar lalata, inda suka rika yiwa farar hula fyade yayin da dakarunsu ke garkuwa da mata a matsayin kwarkwarorinsu a tsawon watanni 18 da aka shafe ana gwabza yaki, a cewar wani jakadan MDD a yau Talata
Yakin na Sudan ya shafi miliyoyin mutane ta fuskar raba su da muhallansu, haddasa karancin abinci da salwantar da rayukan jama'a da dama.
Gwamnatin mulkin sojan kasar Jamhuriyar Nijar ta cimma wata yarjejeniyar kafa wata sabuwar matatar mai da kamfanin Zimar na Canada da nufin samar da wadatar man fetur da iskar gas a kasar da na kasuwanci.
Sanarwar da fadar shugaban kasar Chadin ta fitar tace an kai harin ne kusa da garin Ngouboua dake shiyar yammacin kasar, “inda ya hallaka kimanin mutane 40.”
Rasuwar Hama Amadou da ke matsayin tamkar wani abin ba zata ta matukar girgiza jama’a inda hatta ‘yan siyasar da suka sha karawa da shi a fagen siyasa sun nuna alhini kan mutuwarsa, suna masu kwatanta abin a matsayin babbar asara ga kasa.
A bara ne Amadou da ke hijira a kasashen waje ya koma gida da nufin ba da gudunmowa a kokarin fitar da kasar daga dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Dubban jama'a ne suka taru a ranar litinin a kan titunan birnin Yaounde, suna ta raha don yin maraba da shugaban Kamaru da ya dade ba ya kasar.
Wannan mummunan yanayi ya yi kama da wani lamari makamancin wannan da ya faru a Najeriya makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 140, ciki har da yara kanana.
A ranar litini 21ga Oktoba Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya dawo birnin Yaoundé bayan watani bakwai da barin kasar, inda aka rika yada rade radin mutuwar sa.
Da misalin karfe 5:30 na yamma ne jirgin da ke dauke da Biya da iyalinsa ya sauka a babban filin jirgin saman Nsimalen.
Wasu ‘yan Nijar sun ce har yanzu mahukuntan kasarsu ba su dauki darasi ba, tun katse musu wutar da Najeriya ta yi tsawon watanni 8 bayan juyin mulki a karshen watan Yulin 2023.
Yayin da kasar take dakon sakamakon zaben dake cike da rashin tabbas wanda ya sa ake dada zargin cewa anyi aringizon kuri’u a zaben sannan gwamnatin da ta dade tana mulki a kasar tana kame wadanda suke bayyana ra’ayoyin da suka saba nata.
Domin Kari
No media source currently available