To sai dai a kowane lokaci a arewacin Nijar faya-fan bidiyo na ta yawo a kafafen sada zumunta dake nuna yadda magidanta ke neman ruwa a bakin panpuna inda wasu yankunan suka shafe kwanaki ar’ba’in ba tare da sun samu ruwanba.
Magidanta kan yi tafiya mai nisa domin samun ruwa ga kuma tsada lamarin da matsalar ke neman zama babbar barazana ga al’umma.
Tarin matsaloli, da suka hada da sauyin yanayi da kuma wasu aiyukan gurbata muhalli da wasu al’umma ke gudanarwa na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa wannan matsalar a cewar Sumana Zakariyya shugaban dake kula da samar da albarkatun ruwa na jihar Agadas
Matsalar ruwan sha ta zama wa al’umma a arewacin Nijar karfen kafa lamarin da yassa wasu kungiyoyin farar hula ke duba yiwuwar maka kanfanin dake samar da ruwa a kotu saboda yadda al’umma ke wahala .
A yanzu dai al’umma a wasu yankuna na Nijar sun zubawa sarautar Allah ido suna jiran su ga ranar da za’a rabasu da wannan matsala wacce aka shafe tsawon shekaru ana musu alkawali akai.
Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna