Yanayin murna daya kewaye daga tutar Amirka a ofishin jakadancinta a birnin Havana kasar Cuba ya buge da zama musayar zarge zarge da kakausan harshe tsakanin sakataren harkokin wajen Amirka Jonh Kerry da takwaran aikinsa na kasar Cuba Bruno Rodriguez akan batun kare hakki da 'yancin jama'a.
Bayan fiye da watanni biyu da kaddamar da majalisun tarayyar Najeriya, majalisun basu yi zaman da ya kai na makonni uku ba biyo bayan rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyar APC mai mulki.
Hadakar kungiyoyin mata Musulmi ta gudanar da taron fadakarwa a jihar Gombe ganin yadda ‘yan ta’adda suke amfani da suturar mata Musulmi wajen kai hare haren kunar bakin wake.
Ma'aikatar Tsaron Amurka ta fara gwada ingancin wani sansanin soji a Leavenworth na jahar Kansas, don yiwuwar kai fursunonin soji, wadanda a yanzu ke gidan yarin Guantanamo Bay, na kasar Cuba
Kungiyar lauyoyi ta kasa a Najeriya tace zata ladabtar da lauyan tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso idan yar korafin da kotu tayi ya tabbata.
Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta bullo da sabon salo wajen fafatwa da kungiyar Boko Haram, bayan umurnin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba ta jiya Alhamis cewa, ta kassara kungiya mai tsattsauran ra'ayin addinin cikin watanni uku masu zuwa.
Kimanin maniyyata aikin Hajji dari hudu da sittin ne suke neman gwamnatin njahar Filato ta mayar masu da kudaden da suka biya tun shekara da ta gabata domin zuwa sauke farali.
Kungiyar masu Biredi ta yankin arewacin Nigeria Sun yi babban taron ta a Minna jahar Nejan Najeriya
Taken wannan shekarar ya ta’allaka ne akan harkokin inganta rayuwar jama’a.
Amirka ta yi Allah wadai da harin da aka kai kasuwar Sabon Gari a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria
A wannan wata za'a kawo karshen wa'adin cimma muradun wannan karni na kawar da fatara., ba tare cimma bukatun da aka yi niya ba
Ranar Matasa, rana ce mai muhimmanci ga matsanan duniya ga baki daya, domin ranar ce da za'a tabbbatarwa duniya cewa an bar matasa a baya.
Domin Kari