A jahar Filaton Najeriya kuma, wata sabuwar dambarwa ce ta taso, a yayin da wasu maiyyata aikin hajji su fiye da dari hudu suka koka matuka dangane da yanayin da suka sami kansu na tsaka mai wuya bayan sun bada kudaden su domin tafiya ibada tun shekarar da ta bagata.
Maniyyatan sun bada bayanin cewa sun biya kudi da niyyar tafiya domin sauke farali, sai kuma aka ce masu kudin sun yi batan dabo a lokacin mulkin tsohuwar gwamnatin da ta shude.
Alhaji Mukhtar Nayaya shugaban kungiyar maniyyatan a tattaunawar su da Madina Dauda, ya yi karin bayanin cewar maiyyatan sun biya kudin su tun shekarar da ta gabata ne, kuma sun mika koken su a rubuce, sai kujeru talatin kadai aka basu kuma hakan ya haifar da matsala kwarai wajan rabon kujerun.
Shugaban ya kara da cewar sun yi tattaki tare da wasu daga cikin jama'ar da abin ya shafa zuwa jama'at Nasrul Islam inda aka yi kuri'a aka rabar da waddan nan kujeru da ke kasa, sauran kuma aka ce za'a dawo mana da kudaden kuma an fara bamu wanda hakan ya sa muka tabbatar da sa hannun gwamnati a ciki kuma mun yarda ne saboda bamu da yadda zamu yi.
Shi kuma shugaban hukumar Alhazan Injiniya Danlami Abdullahi Muhammed cewa ya yi, magabatan su ne su ka yi batan dabo da kudin kusan Miliyan dari biyu da Sittin. Ya kara da cewa akwai kwamitin da ya bincika kuma ya gano cewar abin ya zama tamkar wata al'ada ce a wanna ofishin, ko ka biya kudin ka baka da wani tabbacin tafiya sai shekara ta zagayo.
A halin yanzu dai kamar yadda shugaban ya bayyana, kudaden da mutanen nan suka biya basu ba labarin su kuma mun bincika sunayen mutanen da suka bada kudaden su mun tabbatar cewar sun biya.
Ga rahoton Madina Dauda.