Bayan dinke wannan Baraka ne majalisun suka sake lale wajen maida hankali kan abinda suka ce yana ciwa talakawa tuwo a kwarya. Tare da cin alwashin marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a yunkurinshi na ganin ya cimma burinsa na yaki da cin hanci da rashawa da bunkasa kasa.
Ko da yake ana ganin an sami masalaha a majalisar ganin yadda aka rika tada jijiyar wuya da kuma ba hammata iska a farkon tafiyar majalisar, wadansu ‘yan majalisar sunce har yanzu tana kasa tana dabo sai dai kasancewarsu dattawa, zasu ci gaba da kokarin ganin an gyara.
A cikin hira da Muryar Amurka ‘yan majalisa da dama sun bayyana kudurin majalisar na tunkarar matsalolin da suka addabi talakawan kasar, musamman matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya inda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da tada kayar baya.
Wakiliyarmu Madina Dauda na dauke da ci gaban rahoton.