Sansanin na Leavenworth da wani sansanin sojin kuma da ke Charleston, na Jahar South Carolina su ne wurare biyu da Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter ya ba da umurnin a gwada ingancinsu, a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar ta Tsaro. Yayin da jami'an sojin su ka fara gwada dacewar sansanin na Leavenworth jiya, shi kuwa na Charleston sai sati mai zuwa, a bayanin da jami'in ya yi ma Muryar Amurka.
Ana bukatar kai 50 daga cikin fursunonin a sansanin da ke Amurka, a cewar wani jami'in Ma'aikatar Tsaron Amurka. A yanzu haka akwai fursunoni 116 a gidan yarin Sansanin Sojin Ruwan Guantanamo Bay. Da yawa daga cikinsu kuma sun cancanci a kai su wasu kasashen.
Jami'in ya ce jami'an sojin za su kuma duba yiwuwar gwada wasu karin sansanonin soji da na farar hula, don sanin ko za a iya kai fursunonin soji a wuraren cikin abin da ya kira "yanayi na mutunci da tsaro."
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron ta Pentagon Capt. Jeff Davis ya fadi a farkon wannan satin cewa da yiwuwar Ma'aikatar ta Pentagon ta mika ma Majalisar Tarayyar Amurka tsarin shirin rufe gidan yarin Guantanamo Bay wani lokaci bayan Majalisar ta dawo daga wani hutun Agusta.