Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Kakausan harshe Amirka ta yi Allah wadai da harin da aka kai kasuwar sabon gari a arewa maso gabashin Nigeria


Harin kunar bakin wake a wata kasuwa
Harin kunar bakin wake a wata kasuwa

Amirka ta yi Allah wadai da harin da aka kai kasuwar Sabon Gari a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria

Da kakausan harshe Amirka ta yi Allah wadai da harin bam da aka kai wata kasuwa dake da cunkoson jama'a a jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria a ranar Talata daya kashe akalla mutane 47.

A wata sanarwa mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amirka, John Kirby ya lura da cewa, a yayinda babu wata kungiyar data bugi kirgin cewa ita keda alhakin kai harin, an kai harin ne a yankin da yan Boko Haram suka kashe dubban mutane a yan makonin da suka shige.

Yace Amirka tana yiwa iyalai da yan uwan wadanda harin ya rutsa dasu ta'aziya da jaje. Yace Amirka zata ci gaba da goyon bayan yunkurin da Nigeria ta ke yi na kama wadanda keda alhakin kai hare hare na yanzu da da, domi a hukunta su. Yace kamar yadda Amirka ta fada a baya, mazauna arewacin Nigeria sun cancanci gudanar da rayuwa cikin yanci ba tare da tarzoma ko razasnawa ba.

Bam din ya tashi a a kasuwar Sabon gari, a yayinda yake cunkushe da masu cin kasuwa da yammacin Talata.

Duk da ba wanda ya dauki alhakin kai wannan harin, amma jami’an tsaro sun ce ana zargin ‘yan boko haram ne da wannan aika-aikar.

A yan shekarun nan dai ‘yan kungiyar na ta kai mugayen hare-hare da yin garkuwa da jama’a da kuma harin kan mai uwa da wabi.

Ko a ranar lahadin da ta gabata sai da ‘yan boko haram din suka kashe mutane 4 tare da sace wasu mutanen guda 5

XS
SM
MD
LG