Kungiyar kwato 'yancin bil adama ta gudanar da taro a kan muzgunawa dan adam da ake yi a duniya, musamman a nahiyar Africa inda lamarin ya fi kamari.
Rahottani daga kasar Sudan ta Kudu na cewa yanzu haka akwai mutane sun kai 30,000 da ke dab da fuskantar halaka daga matsanaciyar yunwa ta innali-Lah dake addabar wannan kasar
Wannan harin ya faru ne da asubayi ya’u yayin da kuma jiya ne sabon Gwamnan jahar Diffa Abdu Kaza ya fara aiki
Yayin da ake harmar rajistar Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya, ana samun banbancin ra'ayi game da rajistar.
Shugaban kasar Guinea Alpa Conde ya sani nasarar ci gaba da wa'adin mulki na biyu bayan samun kuri'un da zasu hana zuwa zagaye na biyu.
A jamhuriyar nijer yayinda aka cika makwanni ukku da faruwar turereniyar MINA wadda ta hallaka daruruwan alhazai kwamitin dake bin diddigin wannan al’amari domin tantance alhazan nijer da abin ya rutsa da su ya bada rahoton bincikensa.
Kungiyar Boko Haram ta sake salon kai hare hare, tare da yin shigar 'yan banga domin badda kama da nufin yaudarar al'umma su kai hare hare.
Wata Kididdiga da cibiyar bincike kan sha’ainin abinci ta kasa da kasa ta yi, ta nuna cewa kasashen masu tasowa guda 52 ne ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa, kamar yadda alkaluman da ke nuna matsalar ta yunwa na Global Hunger Index suka nuna.
Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar goma sha biyar ga watan Oktoba a matsayin ranar matan karkara ta duniya. Ranar da ake jawo hankalin al’umma kan kalubalan da matan karkara ke fuskanta.
Shugaban Amurka Barack Obama zai tura jami’an sojin Amurka kasar Kamaru, domin sa ido ta sararin sama kan mayakan Boko Haram.
Tsohon gwamnan farin kaya na farko a jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha ya rasu jiya a asibitin koyarwa na jami’ar Patakwal sakamakon bugun zuciya.
Masu kada kuri’a sun yi layi a kasar Guinea yau lahadi da safe domin zaben shugaban kasa, inda shugaban kasar Alpha Conde ya sake tsayawa takara domin neman wa’adin mulki na biyu, tare da ‘yan takarar jam’iyun hamayya bakwai.
Domin Kari