Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hajj: Kwamitin Bincike Ya Mika Rahoto A Nijar


 Saudi
Saudi

A jamhuriyar nijer yayinda aka cika makwanni ukku da faruwar turereniyar MINA wadda ta hallaka daruruwan alhazai kwamitin dake bin diddigin wannan al’amari domin tantance alhazan nijer da abin ya rutsa da su ya bada rahoton bincikensa.

A yayin wani taron manema labaran da suka kira a yammacin juma’a membobin kwamitin da ke bin diddigin abubuwan da suka biyo bayan turmitsitsin na ranar jifan shaidan suka tabbatar da cewa ya zuwa yanzu alhazai ‘yan nijer 78 ne suka rasu.

Shugaban kwamitin Ali Umaru ya kara da cewa yanzu haka ba a san inda alhazai 41 ‘yan nijer suka shiga ba, yayinda aka kyasta cewa mutane 34 da suka ji rauni. Ya bayyana cewa, daga cikin mutane da suka rasu, arba’in da hudu ne kawai aka yiwa takardun rajistar mamata.

Kwamitin ya karyata jita- jitar da ake yayatawa cewa, cikin rami guda aka bunne gawawakin mutanen da suka rasu a turereniyar ta mina. Ya bayyana cewa, an yiwa kowacce gawa sutura yadda ya kamata.

Shugaban kwamitin bin diddigi halin da alhazan nijer suka shiga a yayin wannan iftila’i ya bukaci jama’a su kara hakuri yayinda ake neman karin bayanai kan sauran alhazan da har yanzu ba a tabbatar da halin da suke ciki ba. Bisa ga cewarsa hukumomin Saudiya na ci gaba da tantance ragowar gawarwakin alhazai ta hanyar binciken zanen yatsu domin tantance sunayensu da kasashen da suka fito.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mumuni Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG