Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe 52 Na Fuskantar Matsananciyar Yunwa


Irin barnar da fari ya yi kenan wa gonakin arewa maso gabashin Afirka.
Irin barnar da fari ya yi kenan wa gonakin arewa maso gabashin Afirka.

Wata Kididdiga da cibiyar bincike kan sha’ainin abinci ta kasa da kasa ta yi, ta nuna cewa kasashen masu tasowa guda 52 ne ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa, kamar yadda alkaluman da ke nuna matsalar ta yunwa na Global Hunger Index suka nuna.

Kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ita ce tafi kowace kasa fama da barazanar matsananciyar yunwa a kasashe masu tasowa bisa alkaluman da aka duba da suka hada har da matsalar mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Sannan sai kasashen Chadi da kuma Zambia.

Kididdigar ta gano cewa akwai nasaba tsakanin matsalar yunwa da yake-yake da suka yi fama da su a shekarun baya, da kuma wadanda suke aukuwa a yanzu.

Sannan kididdgra ta nuna cewa a sauran jerin kasashen da ke goman fgarko akwai East Timor, Saliyo da Haiti Madagascar da Afghanistan da Nijar da kuma Yemen, wandandu suma duk suna fusknatr barazanar matsananciyar yunwa.

Dr. Klaus Von Grebmer, mai bincike ne a cibiyar mai lura da sha’anin abinci a duniya, a Berlin, inda daga nan ne aka fitar da wannan rahoto. Kuma a hirar da ya yi da Joe De Capua na sashen Ingilishi na Muryar Amurka ya danganta matsalar da rashin zaman lafiya da wasu kasashe ke fama da su a Afrika.

Yace, “Kasashe biyar cikin takwas na farko daga Afrika ne, kuma cikin wadannan biyar din hudu sun tsinci kansu cikin matsananciyar yunwa saboda yake-yake da a ke yi ko kuma wani abu da ke da nasaba da tashin hankali.”

Dr Klaus ya kara da cewa- “A duk lokacin da aka samu tashin hankali na makamai, manoma, ba za su iya shuka irinsu ba, ko sun shuka ba za a samu daman sayar da sub a, sannan babu damar shigar da kayayyakin da za aikin noma da su, baya ga haka hanyoyin da za a gudanar da kasuwanci duk sukan kasance a rufe. Saoda haka tasirin da yaki ke yi akan haifar da yunwa, babban al’amari ne.”

To sai dai a cewar Dr Klaus idan mahukunta suka himmati, kasashen za su iya saura halin da suka tsinci kansu a ciki.

“Idan masu rike da mukaman siyasa suka maida hankali domin ko a nan Afrika, akwai kasashen da suka yi fama da rikici kuma suka fuskanci wannan matsala da suka da Habasha da Rwanda da Angola, amma kuma daga baya da suka samu zaman lafiya, sai aka maganace matsalar yunwa, na san akwai wuya, amma za a iya yi.”

Ga fasarar rahoton da Sarfilu Hashim ya gabatar

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG