Haruna Bako ya ce Najeriya za ta yiwa Iran ci 2-1 ko kuma ci 2-0
Wasu 'yan Nijer sun ce su duka ne suka yi zanga-zangar lumana a birnin New York, wasu sun ce sam , ban da su a ciki
'Yan ci rani daga sassan Najeriya daban-daban da ke son zama a jahar Enugu su nemi kudi sai sun yi rajistar katin shaida
Majiyoyi da dama daga Najeriya sun tabbatar cewa ‘yan bindiga sun sace Sarkin Uba, Alhaji Ali Ismail Mamza, a lokacin da aka kaiwa jerin gwanon motocinsu hari tare da Sarkin Gwoza da Sarkin Askira Alhaji Abdullahi Ibn Muhammad Askirama.
Wanda ake nema da laifi, kuma wanda ya kira kanshi dan leken asiri da ya tona asirin hukumar tattara bayanan sirrin Amurka, Edward Snowden yace yana so ya dawo gida Amurka.
Kasar Japan tace Koriya ta Arewa ta amince a cigaba da bincike akan mutanen Japan da Koriya ta Arewa ta sace a shekarun 1970 da 1980.
Jami’an kasar Australiya sun tantance cewa jirgin Malaysiannan wanda ya bace, bai fadi a yankin kudancin tekun Indiya ba, inda aka ji alamar karar na’u’ra a watan da ya wuce.
‘Yan aware masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine sun harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar sojin Ukraine, inda sojojin gwamnati 14 ne suka rasa rayukansu, a cikinsu harda wani Janar.
Kwamitin bin diddigi akan daliban Chibok ya isa garin domin ganawa da iyayensu.
Kasar Jordan ta kori Jakadan kasar Syria, wanda hakan ya sa ita ma Syriyar ta rama kan Jakadan kasar ta Jordan.
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa Amurka ta kai makura a Afghanistan, a daidai lokacin da Amurkawa ke kawo karshen yakin da su ke yi a wurin zuwa karshen wannan shekarar.
Paparoma Francis ya gana da Firayim Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu da Shugaba Shimon Peres a jiya Litini, a daidai lokacin da ya ke kammala ziyararsa ta kwanaki uku a gabas ta tsakiya.
Domin Kari