Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Da Koriya ta Arewa Zasu Cigaba Da Sulhu


​Kasar Japan tace Koriya ta Arewa ta amince a cigaba da bincike akan mutanen Japan da Koriya ta Arewa ta sace a shekarun 1970 da 1980.

Firayim minister Shinzo Abe, ya yabawa wannan mataki Alhamis dinnan a matsayin yunkuri na farko wajen kawo karshin lamarin da ya lalata dangantakar Koriya ta Arewa da Japan.

A 2002 ne Koriya ta Kudu ta amince cewa ta sace mutanen Japan su 13 domin su koyawa masu binciken sirrin kasar al-adun Japan.

An mayarda mutum 5 Japan, kuma Koriya ta Arewan tace ragowar duk sun mutu, amma mutane da yawa a Japan na zargin cewa an kara sace wasu su goma sha wani abu.

Wannan mataki na cigaba da binciken, ya zone bayan share kwanaki 3 ana muhimmiyar tattaunawa tsakanin Koriya ta Arewa da Japan a cikin wannan mako a kasar Sweden.

Da yake mayarda da martani, Sakataren Gwamnatin Japan Yoshi-hide Suga yace kasarshi zata sassauta takunkuman da ta sakawa Koriya ta Arewa, idan aka samu cigaba akan batun mutan Japan din da aka sace.
XS
SM
MD
LG