Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma Ya Gana Da Shuwagabannin Addinai


​Paparoma Francis ya gana da Firayim Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu da Shugaba Shimon Peres a jiya Litini, a daidai lokacin da ya ke kammala ziyararsa ta kwanaki uku a gabas ta tsakiya.

Mr. Netanyahu ya gaya ma Paparoma abin da ya sa ya yi imanin cewa Isira'ila na bukatar gina da'irar kariya ma birnin Bethlehem na Yamma da Kogin Jordan. Firayim Ministan na Isira'ila ya ce duk lokacin da aka daina tsangwama da ta'addanci ga Isira'ila ba za a bukaci katangar ba, inda Paparoma Francis ya tsaya ya yi wata addu'a ranar Lahadi.

Mr. Peres ya gode ma Paparoman saboda kokarin da ya yi na farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isira'ila da Falasdinawa wadda ta cije. Paparoma Francis ya gayyaci Mr. Peres da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas zuwa Vatican a watan Yuni don su yi addu'ar zaman lafiya kuma dukkannin mutanen biyu sun anshi goron gayyatar.

Tun da farko a jiya Litini, Paparoma ya ziyarci Dome of Rock (ko Qubba as-Sakhrah) wanda ke a wuri na uku a tsarki a Musulunci, kuma wurin da Musulmi su ka yi imanin cewa Annabi Muhammad ya hau zuwa sammai (wato ya yi mi'iraji). An gina shi wannan Masallacin ne a wuri mafi tsarki ga su ma Yahudawan, wato inda aka yi imanin cewa nan ne aka fara gina masujjada ta farko da ta biyu, kamar yadda ya ke a Littafi Mai Tsarki.

A yayin wannan yada zangon, Paparoma Francis ya yi kira ga mabiya addinan Musulunci da Yahudanci da Masihiyya su rinka girmama juna tamkar 'yan'uwa, ba tare da bata sunan Allah ba ta wajen tayar da hankula.

Paparoma ya kuma tsaya a Western Wall (ko kuma Bangon Kuka) inda ya sunkuyar da kai don wata addu'a ta 'yan mintoci. Wannan Bangon shi ne abin da ya rage na Masujjadar ta biyu, kamar yadda ya ke a Littafi Mai Tsarki, kuma shi ma wuri ne mafi tsarki na addu'ar Yahudawa.
XS
SM
MD
LG