WASHINGTON, DC —
Jahar Enugu ta kaddamar da wani sabon tsarin da ya sa baki 'yan ci rani daga arewacin Najeriya yin rajistar mallakar katin shaida kafin su ci gaba da harakokin su na neman kudi a jahar ba tare da wata tsangwama ba. Wakilin Sashen Hausa a yankin Niger Delta Lamido Abubakar Sokoto yayi tattaki zuwa jahar ta Enugu, inda ya fara zantawa da Alhaji Haruna Sule Sarkin Hausawan Enugu wanda ya yiwa tambayar neman dalilin daukan irin wannan mataki na yiwa 'yan arewa rajistar mallakar katin shaida.
Abubakar Lamido Sokoto ya kara da cewa kudin yin katin shaidar Naira dubu daya ne.
'Yan ci rani daga sassan Najeriya daban-daban da ke son zama a jahar Enugu su nemi kudi sai sun yi rajistar katin shaida