Wanda ake nema da laifi, kuma wanda ya kira kanshi dan leken asiri da ya tona asirin hukumar tattara bayanan sirrin Amurka, Edward Snowden yace yana so ya dawo gida Amurka.
Kasar Japan tace Koriya ta Arewa ta amince a cigaba da bincike akan mutanen Japan da Koriya ta Arewa ta sace a shekarun 1970 da 1980.
Jami’an kasar Australiya sun tantance cewa jirgin Malaysiannan wanda ya bace, bai fadi a yankin kudancin tekun Indiya ba, inda aka ji alamar karar na’u’ra a watan da ya wuce.
‘Yan aware masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine sun harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar sojin Ukraine, inda sojojin gwamnati 14 ne suka rasa rayukansu, a cikinsu harda wani Janar.
Kwamitin bin diddigi akan daliban Chibok ya isa garin domin ganawa da iyayensu.
Kasar Jordan ta kori Jakadan kasar Syria, wanda hakan ya sa ita ma Syriyar ta rama kan Jakadan kasar ta Jordan.
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa Amurka ta kai makura a Afghanistan, a daidai lokacin da Amurkawa ke kawo karshen yakin da su ke yi a wurin zuwa karshen wannan shekarar.
Paparoma Francis ya gana da Firayim Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu da Shugaba Shimon Peres a jiya Litini, a daidai lokacin da ya ke kammala ziyararsa ta kwanaki uku a gabas ta tsakiya.
Mutumin da ake kyautata zaton shi zai zama zababben Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce ba babu wani zancan tattaunawa da wadanda ya kira "'yan ta'adda" wanda wannan shi ne yadda ya kan bayyana 'yan aware magoya bayan Rasha masu dauke da makami.
Wata kotu kasar China ta samu wani rikakken attajirin kasar China da laifin yi kisa a saboda haka ta yanke masa hukuncin kisa.
Kotun kasa da kasa, ICC ta yankewa tsohon shugaban yan yakin sa kai na kasar Congo Germain Katanga hukuncin dauri shekaru goma sha biyu a gidan yari, a saboda rawar daya taka a kisan kiyashin da aka yi a shekara ta dubu biyu da uku.
A Afghanistan wasu yan bindiga dauke da makamai sosai sun budewa ofishin jakadancin Indiya a yammaci kasar wuta a yau juma'a, to amma dukkan ma'aikatan jakadancin sun tsalaka rijiya da baya domin babu wanda yaji rauni.
Domin Kari