Jami’an Gwamnatin kasar Girka sun bada rahoton cewa wasu kananan jiragen ruwan fito biyu dake dauke da dimbin masu kaura sun yi hatsarin kifewa a tsibirin Samos, mutane biyu ne suka halaka.
Rahotannin dake fitowa daga Sudan na cewa rundunar sojin Sudan ta Kudu sun gwabza fada da mayakan ‘yan tawaye a garin nan mai albarkatun main a Benitu safiyar Litinin dinnan.
Jami'ai a Hong Kong sun fara neman wadanda hadarin jirgin ruwa ya shafa.
Shiga Abuja zai yi wuya a ranaku uku da za'a yi ana gudanar da taro akan tattalin arziki na duniya a babban birnin Tarayya.
A jajiberen soma taron tattalin arzikin duniya da za'a yi a Abuja jami'an kasar Najeriya suna sake jaddada cewa hada-hadar kasuwar hannayen jari na nan tana cigaba duk da hare haren bamabamai kusa da babban birnin.
Har yanzu ana ta ci gaba da samun kiraye-kiraye ga shuwagabanni da masu ruwa da tsaki a jagorancin Najeriya da su dukufa domin nemo dalibannan da ke ci gaba da garkuwa da su wadanda aka diba daga garin Cibok.
Ma'aikata a sassan duniya sun hau tituna Alhamis dinnan don bukukuwan zagayowar ranar Ma'aikata ta kasa da kasa da ake kuma kiranta Ranar Watan Mayu, inda su ka yi ta maci tare da kiraye kirayen a kara albashi a kuma kyautata yanayin aiki.
An dage karar da Manjo Al-Mustapha ya shigar game da zargin kazafin shirin kisan Gillar da Sheikh Sanusi Khalid Yayi Masa.
Rahotanni na cewa harkokin yau da kullum sun tsaya Cik a Isra’ila yau litinin da safe, a dalilin bikin tuna zagayowar kisan gillar da aka yiwa Yahudawa miliyan shida a lokacin yakin duniya na biyu.
Wata Kotu a kasar Misra, ta yanke hukuncin kisa a kan ‘yan kungiyar ‘yanuwa Musulmi da ake kira Muslim Brothers su wajen 683 saboda samunsu da laifin aikata kisan wani babban jami’in dan sanda.
Fadar Shugabar Koriya Ta Kudu Park Geun-Hye ta ce Shugabar za ta amince da murabus din Firayim Minista, to amma sai an shawo kan matsalolin da su ka biyo bayan hatsarin jirgin ruwan Sewol.
Paparoma Francis ya ayyana John da John Paul a mastayin waliyyai.
Domin Kari