Shugaban Majalissar Sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani na ziyarar aiki ta wuni 1 a kasashen Mali da Burkina Faso a wannan Alhamis 23 ga watan Nuwamba.
Hukumomin Mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadi game da hukuncin kotun kasashen yammacin Afrika rainon Faransa UEMOA ta yanke dangane da bukatar janye takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar din da na ECOWAS a washe garin juyin Mulkin 26 ga watan Yuli.
Dakarun tsaron jamhuriyar Nijar sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda sakamakon wata arangamar da suka yi a gundumar Sanam ta jihar Tilabery. Lamarin ya faru ne ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba jim kadan bayan da ‘yan bindigar suka kona wata makarantar boko a kauyen Maichilmi.
Kotun daukaka kara ta birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta fara zaman shari’ar da ke tsakanin gwamnatin kasar da Janar Salou Souleyman wanda aka garkame a gidan yari a watan Disamban 2015 tare da wasu hafsoshin soja da fararen hula a bisa zargin yunkurin juyin mulki, zargin da suka sha musantawa.
Hukumomin mulkin sojan jamhuriyar Nijer sun taya takwarorin aikinsu na Mali murnar samun nasarar sake kwato garin Kidal daga hannun ‘yan tawayen arewacin kasar.
Kungiyar matasan lauyoyi ( AJAN) a Jamhuriyar Nijar ta nuna damuwa game da yawaitar kame -kamen mutane tare da tsare su ba a kan ka’ida ba duk da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yulin 2023 sun sha alwashin mutunta yarjeniyoyin kasa da kasar da Nijar ta saka hannu.
Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa an fara cin karfin ayyukan kwashe dakarun Faransa daga kasar ta Nijar.
A jamhuriyar Nijar yau wasu ‘yan kasar, da hadin gwiwar al’ummomin kasashen yammacin Afrika mazauna kasar, su ka yi zaman darshan a harabar kungiyar CEDEAO ta birnin Yamai da jan hankulan shugabannin kasashen yankin kan bukatar su janye takunkumin da suka kakaba bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Kungiyoyin farar hula sun yi gangami ranar Lahadi a birnin Yamai da nufin nuna bukatar mahukunta su kadammar da farautar mukarraban gwamnatin PNDS Tarayya, cikinsu har da shugaba Issouhou Mahamadou da suke zargi da handamar dukiyar kasa, sai dai magoya bayan tsohon shugaban sun yi watsi da batun.
A yayin da wasu ke kyautata zato game da aniyar sabbin jami’an hukumar yaki da cin hanci kan batun yaki da mahandama dukiyar jama’a, wasu na ganin da dama daga cikinsu ba su da kwarewa a wannan fanni mai cike da sarkakiya, a saboda haka suka shawarci hukumomi da su hanzarta magance wannan matsala.
Gwamnatin mulkin sojan Nijer ta gargadi ‘yan kasar su kasance masu nuna halin dattako ko kuma su fuskanci fushin hukuma bayan da tace ta lura da yadda wasu ke yada manufofin kabilanci da na jihanci a kafafen sada zumunta.
Kungiyoyin malaman makaranta a Jamhuriyar Nijer sun fara nuna fargaba bayan da ‘yan bindiga suka abka wata makarantar boko suka yi awon gaba da malamai 2 a wani kauyen jihar Tilabery.
Kwamitin sulhu na kungiyar tarayyar Afrika ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar inda har yanzu babu wani takamaiman jadawalin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiya.
Hukumomin shari’ar jamhuriyar Nijar sun sanar cewa binciken da suka gudanar ya bada damar gano wasu karin bayanan da ke gaskanta zargin yunkurin tserewar shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa. Sun ce sun kama kudade da dama da wasu tarin kayayaki a fadar ta hambararren shugaban.
Wadansu kungiyoyin fararen hula masu goyon bayan sojojin CNSP a Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda suka ce gwamnan Yamai ya na masu katsalandan a harkokin cikin gida.
Kungiyoyin dai na zargin wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka da jefa al'umar Nijar cikin kangin wahalhalu sanadiyyar takunkuman da aka kakaba mata.
Domin Kari