Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yi Zaman Nazarin Hanyoyin Yiwuwar Cire Wa Bazoum Rigar Kariya


Hambararren Shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren Shugaban Nijar Mohamed Bazoum

Wata kotun birnin Yamai ta yi zama a yau juma’a 5 ga watan Afrilu ta 2024 da nufin nazari akan bukatar cire wa hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, rigar kariya a wani yunkurin gurfanar da shi a gaban koliya a bisa zargin cin amanar kasa.

YAMAI, NIJAR - A karshe kotun ta ayyana ranar 10 ga wata a matsayin ranar za ta bayyana hukuncin da za ta yanke.

Kotun ta Cour d’Etat mai mambobi kimanin 22, a zaman da ta yi a karkashin shugabancin Mai Shara’a Abdou Dangaladima a wannan juma’a 5 ga watan Afrilu ta maida hankali ne kan bukatar da Ofishin Ministan Shari’a ya gabatar a madadin gwamnatin Nijar saboda ganin ta cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya a matsayin matakin share fagen shirye-shiryen gurfanar da shi gaban kuliya sanadiyar zargin cin amanar kasa.

Kusa a kungiyar fafutika ta ROTAB Mahamadou tchiroma Aissami na cewa bai ga matsala ba tattare da wannan mataki.

Lauyoyin hambararren shugaban kasar wadanda Me Moussa Coulibaly ya wakilta a wannan zama, sun bukaci kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokacin na gaba ta yadda za su sami damar binciken takardun shari’ar, su kuma gana da mutumin da suke karewa.

Sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba domin alkalan kotun sun ayyana ranar 10 ga watan Afrilun dake tafe a matsayin ranar da za ta sanar da hukuncin da za ta yanke.

Magoya bayan Shugaba Bazoum irinsu Sahanine Mahamadou da ke ganin rashin cancantar hanyoyin da aka bi a yunkurin gurfanar da hambararren shugaban kasar ta Nijar na fatan ganin za a yi adalci a wannan harka.

Sakin Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa da ma mukarraban gwamnatinsa na daga cikin sharudan da kungiyoyin kasa da kasa da manyan kasashen duniya suka gindaya wa hukumomin mulkin sojan Nijar kafin su sake mayar da cikakkiyar hulda da wannan kasa yayinda mahukuntan kasar ke cewa abin na da kamar wuya saboda girman laifin da suke zarginsa da aikatawa.

A baya kotun CEDEAO ta umurci a sallame shi sai dai abin bai yi tasiri ba dalili kenan tun daga wancan lokaci kawo yau magoya bayan Shugaba Bazoum ke fassara matakin ci gaba da tsare shi a matsayin bita da kullin siyasa.

A saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

Kotu Ta Yi Zaman Nazarin Hanyoyin Yiwuwar Cire Wa Bazoum Rigar Kariya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG