NIAMEY, NIGER - Wannan na zuwa ne washe garin wata hirar da shugaban majalissar CNSP Janar Abdourahamane Tiani ya ce ya yi ta waya da Vladimir Putin game da huldar Russia da Nijar.
A yayin ganawar da aka yi a tsakanin Ministan Cikin Gida, Janar Toumba Mohamed da jakadiyar Amurka a Nijar, Kathleen Fitzgubbon, a wannan Laraba 27 ga watan Maris ne jami’an kasashen biyu suka tattauna kan sanarwar da hukumomin mulkin sojan Nijar suka bayar a ranar 16 ga wata wacce a ciki suka bayyana yanke shawarar tsinke huldar ayyukan soja da kasar Amurka saboda abinda suka kira rashin gamsuwa da halaccin yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma a shekarar 2012 a wani bangare na karfafa matakan yaki da ta’addanci.
A bayyane take sanarwar gwamnatin rikon kwaryar ta Nijar tamkar umurni ne akan bukatar Amurka ta kwashe dakarun 1100 da ta girke a arewacin kasar.
Abin da ya sa jakadiya Kathleen Fitzgubbon a ganawarta da ministan cikin gidan Nijar Janar Toumba ta sanar da shi cewa Amurka ta yi na’am da matakin da Nijar ta dauka saboda haka kasar za ta gabatar da wani daftarin da bangarorin biyu za su tattauna kansa domin tsara jadawalin kwashe sojojin na Amurka daga kasa kamar yadda aka wallafa a shafin yanar gizo na ma’aikatar cikin gidan jamhuriyar Nijar.
Jakadiyar Amurka ta jaddada cewa kasarta za ta ci gaba da tallafawa al’ummar wannan kasa kamar yadda aka saba ta hanyar ayyukan raya karkara a karkasin inuwar hukumar USAID.
Kafafen gwamnatin Nijar a ranar Talata 26 ga watan Maris sun sanar cewa bayan yi wa juna jaje da barka ta wayar tarho, Janar Abdourahamane Tiani da Vladimir Putin na Rasha, sun tattauna ne kan hanyoyin karfafa huldar kasashen biyu abin da ke kara fayyace kusanci da aka fara samu a tsakaninsu.
Tallafin Amurka ga jamhuriyar Nijar a fannin tsaro wani abu ne da za a kiyasta akan milioyiyin daloli a kowace shekara. Magana ce ta gudunmowar makamai da na’urori da motocin soja, bayanan sirri da horo har da manyan jiragen dakon sojojin samfarin C130 da a yanzu haka ke taimaka wa sha’anin tsaro a Nijar har ma da wasu kasashe makwabtanta.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna