Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Dokar Bada Kwangilar Gwamnati A Nijar Ta Fara Tada Kura


Janar Abdourahmane a Yamai, Nijar - REUTERS/Balima Boureima.
Janar Abdourahmane a Yamai, Nijar - REUTERS/Balima Boureima.

Hukumomin mulkin sojan jamhuriyar Nijar sun soke harajin kayayyakin da aka yi oda domin amfanin jami’an tsaro da na fadar Shugaban Kasa da na gidaen manyan jami’an gwamnati da wadanda suka shafi tallafin ‘yan gudun hijirar cikin gida.

NIAMEY, NIGER - Matakin wanda za a zartar da shi a tsawon wa’adin mulkin rikon kwarya na bai wa hukumomin hurumin bada irin wadanan kwangiloli ba tare da bin hanyoyin da dokar kula da kwangiloli da odar kayayakin gwamnatin kasar ta tanada ba, lamarin ne dake haddasa shakku a zuciyar wasu ‘yan kasar.

Kafuwar majalissar CNSP da matakin soke kundin tsarin mulkin kasar Nijar da wasu mahimman matakan da suka biyo baya a washe garin juyin mulkin da aka fuskanta ne aka zayyana a takardar da shugaban majalissar CNSP, Janar Tiani, ya saka wa hannu domin bullo da dokar da ke bai wa mahukuntan rikon kwarya dama kai tsaye su yi odar kayayyaki ko bada kwangiloli da ayyukan da suka shafi ma’aikatar tsaro da fadar shugaban kasa da batun kula da ‘yan gudun hijira.

Dan fafutika kuma mamba a kungiyar ROTAB, Mahamadou Tchiroma Aissami, ya ce bai ga matsala ba game da wannan mataki.

Sabuwar dokar ta kuma tanadi matakin sauwake biyan haraji wa irin wadanan kwangiloli a tsawon wa’adin mulkin rikon kwarya, sai dai Shugaban kungiyar farar hula ta FCR, Souley Oumarou, dai bai gamsu da wan tsari ba.

Batun sirrin tsaro na daga cikin dalilan da wasu ‘yan kasa ke bayyanawa a matsayin wata hujjar da za a fake da ita wajen daukan wannan mataki.

To amma reshen Transparency International a kasar Nijar, ta bakin Shugaban kungiyar, Malan Maman Wada, na da shakku kan ainihin dalilin shimfida wannan tsari mai cike da rufa-rufa.

A baya dokokin kasar sun yi tanadin cewa bada kwangilar da darajarta ta kai million 300 na CFA wani abu ne da ya zama dole hukumomi su bada sanarwa a taron Majalissar Ministoci, haka kuma wajibi ne a guji bayar da kwangila a karkashin tsarin daga ni-sai-kai dalili kenan a watan Fabrairun da ya gabata wasu ‘yan Nijar suka sha guna-guni bayan da hukumomin mulkin soja suka yi odar motoci sama da 100 domin amfanin jami’an tsaro wadanda aka kyasta cewa darajarsu ta haura million 4000 na cfa da aka fitar daga asusun tarbacen gudunmowar ‘yan kasa FSSP ba tare da an shawarci jama’a ba.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Wata Sabuwar Dokar Bada Kwangilar Gwamnati A Nijar Ta Fara Tada Kura.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG