Jam’iyyun kawancen hamayya a jamhuriyar Nijer sun lashi takobin ganin an bai wa dan takararsu Mahaman Ousman nasarar da su ke ikirarin ya samu a fafatawar da ta hada shi da Bazoum Mohamed a ranar 21 ga watan Fabrairu sai dai jam’iyyar PNDS mai mulki na cewa a hadu a kotu domin ta raba gardama.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta lashi takobin kawo karshen zanga zangar da aka shafe kwanki uku ana gudanarwa a birnin Yamai, bayan fitar da sakamakon zaben ranar 21 ga wannan wata.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar kama mutane sama da 200 cikinsu har da tsohon kwamandan rundunar mayakan kasar Janaral Moumouni Boureima sanadiyar zanga zangar da ta barke a birnin Yamai sa’o’i kadan bayan da hukumar zabe ta fitar da sakamakon zagaye na 2 na zaben shugaban kasar.
Yau da maraice hukumar zaben jamhuriyar Nijer ta fitar da kammalallen sakamakon zagaye na 2 na zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan fabrerun 2021.
A Jamhuriyar Nijar, an shiga jimamin mutuwar ma'aikatan zabe da suka rasa rayukansu bayan da motarsu ta taka nakiya a yankin Tillabery.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun tabbatar da rasuwar wasu jami’an zabe bakwai kana uku suka ji rauni a ranar Lahadi 21 ga watan Faburairu.
Al’umar Jamhuriyar Nijar ta fita rumfunan zabe don kada kuri’a a zaben shugaban kasa da ake yi zagaye na biyu.
Masana sha’anin tattalin arziki da kungiyoyin kare hakkin mata a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da matakin jaddada tsohuwar ministar kudin Najeriya Dr. Ngozi Okonjo Iweala a matsayin sabuwar shugabar hukumar cinikiyya ta duniya.
Shuwagabannin kasashen G5 Sahel sun kammala taronsu na shekara shekara a jiya Talata a garin N’Djamena, inda suka tattauna hanyoyin da za su bullo wa kungiyoyin ta’addancin da suka addabi al’ummomin iyakokin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso.
Alkali mai kare muradun hukuma (Procureur de la Republique) ya gargadi ‘yan siyasa a Jamhuriyar Nijar su daina amfani da kalaman kabilanci a yakin zaben dake gudana a yanzu haka.
Kungiyoyin mata a jamhuriyar Nijer suna kara neman hadin kan kasa yayinda ya rage kasa da mako 1 a gudanar da zabn shugaban kasa.
Kungiyoyin rajin kare dimokradiyya a jamhuriyar Nijar sun fara yiwa ‘yan kasar hannunka mai sanda bayan la’akari da sabon salon da ‘yan siyasa suka bullo da shi a wannan lokaci na yakin neman zaben shugaban kasar zagaye na biyu.
An shiga cece kuce a Jamhuriyar Nijar bayan da jakadan kasar Faransa ya kai ziyara a gidajen ‘yan takarar da zasu fafata a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar 21 ga watan Fabrairu.
Hukumar zaben jamhuriyar Nijer na ci gaba da tuntubar rukunonin al’umar kasar da nufin tattara shawarwarin da zasu bada damar gudanar da zaben shugaban kasa na ranar 21 ga watan Faburairu cikin kyaukyawan yanayi.
Hukumar sadarwar jamhuriyar Nijer ta soke wata mahawarar da ya kamata a yi ta kafar television mallakar gwamnati da nufin baiwa ‘yan kasar damar jin manufofin kowane daga cikin ‘yan takara 2 da zasu fafata a zaben 21 ga watan fabrerun da muke ciki.
Bazoum Mohamed yace sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki ya yi nuni da cewa jam’iyar PNDS da kawayenta na da rinjaye a sabuwar majalisar dokoki domin muna da kujeru 129 daga cikin kujerun wakilci 166
Jam’iyyun da suka zo na uku da hudu a zagayen farko na babban zaben shugaban kasa a jamhuriyar Nijar, sun bada sanarwar hada kai tare da mara wa dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki baya.
Hukumar yaki da cin hanci a jamhuriyar a Nijer ta bada sanarwar kwato wasu makudan kudaden haraji da suka makkkale a hannun wasu kamfanoni da masana’antun da ake zargi da turjewa ma’aikatar harajin kasar.
Shuwagabanin Hukumar zaben jamhuriyar Nijer sun gana da jakadun kasashen waje da wakilan kugiyoyin kasa da kasa a yau da hantsi domin tantauna hanyoyin da za a tunkari zagaye na 2 na zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar 21 ga watan fabrerun dake tafe.
Kungiyoyin rajin kare dimokradiya sun kaddamar da ayyukan fadakar da jama’a tare da tunatar da masu hannu akan sha’anin gudanar da zabe
Domin Kari