Wannan ya biyo bayan da Fira Minista Ouhoumoudou Mahamadou ya shafe wunin jiya ya na fayyacewa ‘yan majalisar mahimman ayyukan da gwamnatin ke sa ran gudanarwa a tsawon wadanan shekaru domin talakawan kasar.
Mahamadou ya kudiri aniyar baiwa fifiko a manufofin siyasar da ake kira DPG da nufin samar da kwanciyar hankali a kasa matakin da ‘yan majalisa na bangaren rinjaye irinsu Hon Sanoussi Mareni suka ce sun gamsu da shi.
Fannin tattalin arziki, karfafa matakan yaki da cin hanci da samar da shara’a ta gaskiya da matakan bunkasa noma da kiwo don vci gaban karkara na daga cikin batutuwan da Fira ministan ya tabo a jawabinsa.
Haka kuma a wani yunkurin hada kan ‘yan kasa, Fira minista ya ce gwamnati za ta dauki matakin samar da hanyoyin tuntuba tsakanin ‘yan adawa da masu rinjaye sannan za a bullo da wata hanyar da jagororin ‘yan adawa za su rika ganawa da hukumomin koli domin tattauna batutuwan da suka shafi tafiyar kasa.
‘Yan adawa wadanda suka yi amfani da wannan dama wajen caccakar manufofin sabuwar gwamnatin da suke danganawa da shudaddiyar gwamnatin Issouhou Mahamadou, sun ce ba su gamsu ba da bayanan da Mahamadou ya zo da su, domin a cewar Hon Ibrahim Yacouba gwamnatin ta yi tuya ta manta da albasa.
Bayan tafka zazzafar mahawara a tsakanin bangarorin majalisar, masu rinjaye sun yi na’am da tsarin siyasar gwamnatin da kuri’u 129 daga cikin 172.
Sai dai ‘yan adawa sun fice daga zauren majalisar a dai-dai lokacin da ake shirin yin kuri’a domin a cewarsu, ba a kula da bukatun talaka ba a sabuwar tafiyar da ake shirin shimfidawa a kasa.