Akalla mata 700 zuwa 750 ke fadawa cikin matsalar yoyon fitsari a kowace shekara a kasar lamarin da ake alakantawa da dabi’ar aurar da ‘yan matan da ba su kosa ba dalili kenan hukumomi da kungiyoyi suka fara yunkurin karfafa ayyukan waye kan al’uma game da wannan matsala.
Da take jagoranci wani gangami a asibitin kula da mata masu yoyon fitsaro Jagorar yaki da wannan cuta Uwargidan shugaban kasa Mme Bazoum Hadiza Mabrouk ta yi tunatarwa game da matsayar da kasashen duniya ke kanta dangane da wannan cuta.
Mme Bazoum ta ce ‘yancin mata shi ma ‘yancin dan adam ne kamar kowanne, saboda haka ya kamata mu tashi tsaye don yakar cutar yoyon fitsari.
Ta kara da cewa, tana kira ga dukkan masu hannu a wannan yaki su tashi tsaye don ganin ana kawar da wannan cutar kwata-kwata daga kasar.
Ganin yadda wannan matsala ke kara tsananta a nan Nijar ya sa hukumomin lafiya samar da karin kayan aikin tiyatar mata masu yoyon fitsari a cibiyar CNRFO dake birnin Yamai yayin da a nan gaba kadan ake shirin daukan irin wadanan kayan aiki a Maradi.
Mata masu yoyon fitsari kan yi fama da kyama daga al’uma har ma wasu dangi da mazajensu abinda ke jefa su cikin halin damuwa. Domin karawa irin wadanan mata kwarin guiwa su tunkarikalubalen rayuwa kungiyar CODECO mai zaman kanta ta bude wani sashen koyar da su dinkin tela.
Matan dake karbar magani a cibiyar ta CNRFO sun sha alwashin koyar da ‘yan uwansu mata a karkara yayin da a wani bangare suka kudiri aniyar bada gudunmowa a ayyukan waye kai don riga-kafin cutar ta yoyon fitsari.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: