Sai dai ‘yan rajin kare hakkin dan adam najan hankula akan bukatar a yi adalci don tantance gaskiyar abubuwan da suka faru.
Capitaine Sani Gourouza wanda hukumomin Nijar suka dorawa alhakin harbe-harben da aka yi a kewayen fadar shugaban kasar Nijar kwanaki 2 kafin saukar Issouhou Mahamadou daga karagar mulki, ya fada komar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol ne a farkon mako a Jamhuriyar Benin.
An kama shi ne tare da wasu matasan sojoji da ake zargi da hada kai da shi wajen yunkurin kifar da gwamnati.
Ko da yake ba a bayyana yawansu ba, majiyoyin tsaro sun ce an damka wadannan sojoji a hannun rundunar tsaro ta Gendarmerie Nationale wacce ke da alhakin gudanar da binciken farko akan wannan al’amari.
Hakan ya sa shugabar kungiyar kare hakkin matasa ta JENOM Hajiya Falmata Taya yin tunatarwa akan batun mutunta ‘yancin dan adam.
Tun a ranar da gwamnatin Nijar ta bada sanarwar murkushe yunkurin juyin mulkin 31 ga watan Maris wasu ‘yan kasa ke kallon abin tamkar wani wasan kwaikwayo dalili kenan jami’in fafutuka na gamayyar kungiyoyin Reseau Esperance, Bachar Maman ke shawartar hukumomi su dauki matakin baiwa ‘yan kasa damar sanin irin wainar da za a toya a yayin shara’ar wadannan sojoji.
Da ma tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou a jawabinsa na bankwana da shugaba Bazoum Mohamed a lokacin da yake rantsuwar hawa kujerar mulki, sun sha alwashin damko wadannan sojoji domin gurfanar da su a gaban koliya.
Sai dai masu fafitikar kare hakkin dan adam na cewa ‘’ba girin-girin ba ta yi mai’’.
Saurari rahoto a cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: