An fara aikin ne a daukacin jihohin kasar a ci gaba da tada tsauraran matakan kare al’uma daga wannan annoba da ta addabi duniya.
Mutum kimanin dubu 800 ne ake sa ran yi wa alluran rigakafin coronavirus a yayin wannan aiki da zai kwashe tsawon kwanaki 10, dake zaman na biyu irinsa bayan wanda aka kaddamar a birnin Yamai ranar 29 ga watan Maris din da ya gabata.
Sabanin yadda a wasu kasashe ake samun mutane dake nuna fargabar illolin dake tattare da alluran rigakafin, har ya zuwa yanzu ba a sami korafi daga wasu ba game da sahihancinta a jamhuriyar Nijar.
Hakan na faruwa ne makonni kusan biyar bayan kaddamar da aikin farko dake shafar dubban mutane, a cewar Dakta Adamou Foumakoye Gadon na asibitin kwararu na General de Reference.
Domin tantance yadda mazaunan birnin Yamai suka karbi rigakafin Covid-19 ministan kiwon lafiya ya leka wasu daga cikin cibiyoyin da aka kebe don wannan aiki, fitowar mutane na nunin abin ya sami karbuwa.
A tsakiyar watan jiya ne Jamhuriyar Nijar ta karbi tallafi alluran Astrazeneca 350,000 a karkashin shirin COVAX mai hangen tallafawa kasashe matalauta makonni biyu kenan bayan da hukumomin kasar suka karbi wani tallafin kasar China mai kunshe da alluran SinoPharm 400,000 mafarin kaddamar da wannan aiki a dukkan fadin kasar mai yawan mutum miliya 22.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.