A Jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun fitar da sakamakon jarabawar da suka shirya a watan Nuwamban 2020 domin tantance malaman da suka cacancin aikin karantarwa a makarantun sakandare a ci gaba da daukan matakan farfado da sha’anin ilimi.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun karbi wani ruunin tallafin allurar riga kafin covid 19 samfarin Johnson & Johnson a matsayin wata gudunmowa daga gwamnatin Amurka a karkashin shirin Covax mai amar da riga kafin wannan anoba ga kasashe masu karamin karfi.
An gudanar da taro da nufin kara hada kan mata da ‘yan matan kasar Nijar a ci gaba da karfafa matakan kare hakkin mata musamman a fannin siyasa.
Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta fara gudanar da taron gaugawa bayan da gwamnatin kasar ta bukaci a aiwatar da gyaran fuskar kasafin kudaden 2021 sakamakon sauye sauyen da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ta zo da su.
Dakarun tsaron jamhuriyar Nijer sun hallaka gwamman ‘yan ta’adda a yammacin jiya lahadi lokacin da suka kai hari a kauyen Tchomabangou dake jihar Tilabery koda yake sojoji 4 da fararen hula 5 sun rasu a yayin wannan arangama.
A Jamhuriyar Nijar bangarorin siyasar kasar sun bayyana matsayinsu game da kamun ludayin shugaba Mohamed Bazoum wanda ke cika kwana 100 akan kujerar mulki bayan lashe zagaye na 2 na zaben 21 ga watan Fabrairun 2021.
A Jamhuriyar Nijar masu sarrafa kayan noma da kiyo sun fara gudanar da taro domin tsayar da shawarwarin da za su gabatar a taron hukumar cimaka na birnin Roma da taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a kowane watan Satumba a birnin New York.
A karshen zamanta na shekara shekara majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta shwaraci gwamnatin kasar ta kara jan damara domin kawo karshen aika-aikar ‘yan bindiga da ‘yan ta’addanda suka addabi jama’a.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da gwamnan jihar Borno Farafesa Babagana Umara Zulum sun isa garin Diffa a da hantsin ranar Alhamis inda za su tattauna akan makomar ‘yan gudun hijira.
Ranar daya ga watan Yuli shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ke soma ziyarar aiki a jihar Diffa inda gwamnatin kasar ta kaddamar da ayyukan mayar da ‘yan gudun hijirar cikin gida sama da 200,000 zuwa garuruwansu na asali a ci gaba da karfafa matakan farfado da tattalin arzikin jihar.
Harakoki sun fara dawowa sannu a hankali a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar inda jama'ar yankin ta fara komawa kan ayyukan yau da kullum bayan da aka fara shawo kan matsalar tsaron da aka yi fama da ita a shekarun baya.
Yau talata hukumomin jihar Diffa, Jamhuriyar Nijar, suka jagoranci ayyukan kwashe wasu daruruwan ‘yan gudun hijira zuwa garinsu na asali a ci gaba da daukan matakan farfado da tattalin arzikin jihar bayan shafe shekaru kusan 6 tana fama da hare haren kungiyar Boko Haram.
Kotun ECOWAS ta umurci hukumomin jamhuriyar Nijer su biya diyyar million 50 na cfa domin shafe hawayen wani dan gwagwarmayar kasar da ya shafe watanni 18 a kurkuku bayan da ya kira wani gangamin nuna adawa da dokar harajin kasar a shekarar 2018.
A Jamhuriyar Nijar wata kungiyar kare hakkin jama’a ta bude layin waya da nufin tattara koke-koken jama’a masu nasaba da toye hakkin dan adam.
A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar sun fara maida martani bayan kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a gidan kakakin majalisar dokokin kasar Seyni Oumarou dake birnin Yamai a ranar Asabar 12 ga watan Yuni.
Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta nada tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou da shugaban Nana Akufo Addo na Ghana a matsayin gwarazan tattara kudaden yaki da ta’addanci.
Da yake mayar da martani ga masu korafi akan wannan aiki dan majalisar dokokin kasa Hon. Lawali Ibrahim Mai Jirgi na cewa, bai ga laifi bai idan aka saka ‘yan majalisa cikin kyakkyawan yanayin aiki.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar sake bude iyakokin kasar da nufin baiwa jama’a damar zirga-zirga a tsakanin kasar da kasashe makwafta amma da sharadin nuna takardar shaidar gwajin cutar COVID-19.
Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin baiwa dan gwagwamaryar nan Anas Djibrilla damar ganawa da lauyansa bayan da ya shafe watanni kusan 3 a garkame a gidan kason Koutoukale saboda zarginsa da yunkurin kifar da gwamnati.
kungiyar ROTAB mai fafutukar ganin an yi haske a sha’anin ma’adanan karkashin kasa ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki matakan da za su bada damar rajistar mutanen da ayyukan shimfida bututun man Nijar-Benin zai raba da gonakinsu don ganin ba a manta da kowa ba wajen biyan diyya.
Domin Kari