Jamhuriyar Nijer na daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna a yankin Afrika ta yamma akan maganar bauta a bisa la’akari da bayanan da ke nunin yadda a wasu yankunan kasar ake ci gaba da aikata wannan haramataciyar dabi’a lamarin da ya sa a shekarun baya kungiyar TImidiria da wasu kawayenta suka daura damanar magance wannan matsala, sai dai alamu na nunin har yanzu da sauran rina a kaba inji sakataren kungiyar Ali Bouzou.
Wannan al’amari dake ci gaba da turjewa doka wani abu ne da ke shafar tsarin zamantakewar al’uma inji Masani a wannan fanni Dr Sani Yahaya Janjouna.
Jinsin mata ya fi dandana kudar wannan haramtaciyar dabi’a wace a wani zubin kan shafi rayuwar yaran da matan da suka tsinci kansu cikin halin bauta kamar yadda tamabarar masarautar Keltemet Mme Almansour Hindou ta bayana wa Muryar Amurka.
Dukkan gwa;notocin da suka mulki Nijer sun sha alwashin kawo karshen bauta a wannan kasa ta hanyar dokokin da aka kafa shekaru da dama sai dai kawo yanzu abin na nan kamar a nan magani kai yana kaba lamarin da kungiyar Timidria ta dora alhakinsa akan raunin wadanan dokoki a yayinda hukumomI da kansu ke dari darin shiga wannan yaki gadan gadan gudun kada a sami sabani a tsakaninsu da sarakunan gargajiyar dake ci gaba da bautar da mutane a yanzu haka lamarin da ya sa a kowane lakoci Timidria kan garzayawa kotun ECOWAS a maimakon ta ja shara’a a nan gida,
Saurari cikakken rahaton cikin sauti: