Mohamed Bazoum ya bukaci ‘yan kasar su ba shi lokaci kadan domin zartar da wannan mahimmin kudiri na kwatowa kasa hakkokinta daga hannun barayin biro kamar yadda ya bayyana wa shugaban sashen Hausa Aliyu Mustapha Sokoto.
Shugaban Nijer yace babu shakka kasashen Afrika na fama da wannan matsala ta cin hanci matsalar da ya kudiri aniyar magancewa a Nijer.
Bazoum Mohamed yace ba a fuskantar cin hanci a fannin ma’adanan karkashin kasa sakamakon matakan dake gudanar da wannan fanni amma matsalar ta shafi akasarin fannoni daga jami’an tsaro zuwa fannin ilimi, lafiya, haraji. da dai sauransu.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Babban Kalubalen Da Na Fuskanta A Watanni 7 – Shugaba Bazoum
Nijar Na Bukatar Amfani Da Kudin Bai-Daya Da Najeriya – Shugaba Bazoum
Juyin Mulki A Guinea Bai Zo Da Mamaki Ba – Shugaba Bazoum