Hakan na zuwa ne bayan da ma’aikatar haraji tayi barazanar cin tarar duk wanda aka kama yana sayar da magunguna ba tare da yin amfani da sabuwar manhajar tantance kudaden harajin TVA ba, kamar yadda sabuwar dokar harajin kasar ta yi tanadin yi daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2022.
Rashin samun daidaito game da bukatar karin wa’adin wata 1 domin shiga sabon tsarin biyan kudaden harajin cinikayya wato TVA ya sa kungiyar masu shagunan kemis ta umurci ‘ya'yanta su dakatar da aiki daga wannan Laraba 1 ga watan Disamba da nufin bai wa ma’aikatar haraji damar shigar da manhajar tantance kudaden wannan haraji na TVA a kwamfitocin masu shagunan magunguna, kamar yadda suka bayyana a sanarwar da suka fitar.
A watannin da suka gabata ne ma’aikatar harajin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ‘yan kasuwar kasar sabon tsarin biyan kudaden harajin TVA da ta ke shirin zartarwa daga farkon shekarar dake tafe. Saboda haka ta gargadi dukkan wadanda matakin ya shafa su gaggauta daukar matakan mutunta wannan tsari ko kuma su fuskanci fushin doka.
Tuni dai wannan takaddama ta fara shafar jama’a a birnin Yamai.
To wata sanarwar da aka bayar a dazu na cewa an sami fahimta a tsakanin ma’aikatar haraji da kungiyar masu shagunan kemis ko kuma pharmacie, wacce ta yi kiran ‘ya'yanta su koma kan aiki sakamakon karin wa’adin wata 1 da suka samu daga wajen hukumomi.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma: