A jamhuriyar Nijer Hukumar sadarwa wato CSC ta gargadi kafafen yada labarai akan maganar mutunta ka’idodin aiki don gujewa haddasa rudani a kawunan al’umma a irin wannan lokaci na fama da matsalar tsaro.
A yayinda kwamitocin majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer ke nazari akan kasafin kudaden shekarar 2022, shugabanin kungiyoyin fararen hula a nasu bangare sun fara binciken daftarin kasafin dake gaban majalisar.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bayyana shirin cimma yarjejeniyar odar jiragen yaki da motoci masu sulke daga kasar Turkiya da nufin karfafa wa dakarun kasar gwiwa a yakin da suke kafsawa da ‘yan ta’adda.
Tsohon shugaban kasar Nijar Mahaman Ousman wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya sha kasa a zagaye na 2 na zaben da ya jaddada aniyar bin hanyyoyin lumana wajen gwagwarmayar kwato abinda ya kira galabar da ya samu a wannan zabe.
Shugaban kasar Nijer ya jaddada aniyar karfafa matakan yaki da cin hanci da karbar rashawa ta yadda za a soma hukunta wadanda aka kama da hannu a irin wannan haramtacciyar dabi’a dake zama ruwan dare a Nijer kamar sauran kasashen Afrika.
Shugaban Sashen Hausa ya kammala ziyarar aiki ta mako guda a Jamhuriyar Nijar ya kuma tashi zuwa kasar Kamaru.
Najeriya na daga cikin kasashe masu tasowa dake fama da rashin ingantattun abubuwan kiwon lafiya da hakan ke haifar da yawan mutuwar jarirai da kananan yara musamman 'yan kasa da shekara biyar.
Muryar Amurka ta karrama wasu kungiyoyin ci gaban jama’a da makarantun koyon sana’a a jamhuriyar Nijer sakamakon gudunmowar da suke bayarwa wajen samarda ci gaban al’uma musamman batutuwan da suka shafi mata da matasa.
A ci gaba da ziyarar aikin da ya fara a jamhuriyar Nijar, shugaban sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha ya jagoranci wata mahawarar bainar jama’a a birnin Yamai.
A jamhuriyar Nijer shugabanin kungiyoyin kwadago da na kungiyoyin fararen hula sun fara gudanar da taro domin nazarin hanyoyin magance matsalolin dake damun matafiya akan hanyoyin zirga zirgar kasashen Afrika ta yamma.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya yi rangadi a karshen mako a gundumar Banibangou don jajantawa al’umma rasuwar wasu mutane kimanin 69 cikinsu har da magajin gari wadanda ‘yan ta’adda suka yi wa kwanton bauna a farkon mako.
Wani harin da aka kai a karkarar Anzourou ta jihar Tilaberry a cikin dare, alhamis wayewar jiya juma’a ya yi sanadin mutuwa sojojin Nijer da dama.
Gwamnatin jahuriyar Nijer ta ayyana zaman makokin kwanaki 2 daga yau juma’a 5 ga watan Nuwamba biyo bayan mutuwar mutane kimanin 69 a gundumar Banibangou ta jihar Tilabery cikinsu har da magajin gari bayan da ‘yan ta’adda suka yi masu kwanton bauna.
Wadansu gwamman ‘yan sa kai don samar da tsaro a gundumar Banibangou ta jihar Tilabery a jamhuriyar Nijer, cikinsu har da magajin gari sun yi batan dabo bayan da ‘yan bindiga suka yi masu kwanton bauna a yayinda suke sintiri a kewayen gari.
A yayinda ake wuni na 2 na taron sauyin yanayi a birnin Glasgow na kasar Birtaniyya wasu kwararu daga jami’oin kasashen Sahel sun fara gudanar da taro a jamhuriyar Nijer.
Wata kotun birnin Yamai ta sallami Ali Tera, wani fitaccen mai hamayya da gwamnatin shugaba Issouhou Mahamadou, dan Nijer mazaunin kasar Amurka da hukumomin Nijer suka yi nasarar tuso keyarsa a shekarar 2019 suka kuma garkame shi a gidan yari.
A shekarun baya birnin Yamai na daga cikin manyan biranen da ake sakawa a jerin wadanda ke da cikakken tsaro a yankin Afrika ta yamma.
Kungiyar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta sanar cewa dubban mazaunan yankin Tilabery na cikin yanayin yiyuwar fuskantar barazanar karancin abinci sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro, inda ‘yan ta’adda suka hana gudanar da aiyukan noma a damunar da ta gabata.
Domin Kari