Lauyar ta bayyana damuwa ne a game da makomar wadannan mutane da kuma yadda abin ka iya shafar darajar kasar Nijar da ta Majalisar Dinkin Duniya a idon masu kare hakkin dan adam.
Rashin samun amsa mai gamsarwa daga wajen mahukunta da kuma yadda kotu ta yi watsi da dukkan kararrakin da aka gabatar mata kan bukatar soke kudirin korar wadannan ‘yan Rwanda 8 da suka sami mafaka a Nijar bayan wata yarjejeniya da aka cimma a tsakanin hukumomin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ya sa lauyar da ke kare su Me Kadidjatou Hammadou kiran taron manema labarai don sanar da duniya halin da ake ciki a yayin da ya rage kwana guda wa’adin da mahukuntan Nijar suka basu zai cika.
Wannan al’amari da tuni ya fara daukar hankalin lauyoyi sama da 100 daga sassa dabamdaban na duniya abu ne da ka iya shafa wa Nijar kashin kaji akan batun kare hakkin dan adam ganin yadda mutanen da ake dambarwa akansu tsofaffi ne, matashinsu shine mai shekaru 60 inji Me Kadidjajtou Hammadou.
Lauyar ta kara da cewa wadannan mutane duk da kasancewar an same su da hannu a yakin basasar shekarar 1994 kotu ta wanke wasu daga cikinsu yayin da wadanda aka kama da laifi suka riga suka kammala zaman hukuncin da aka yanke masu.
Sai dai watanni kusan 2 da barkewar wannan dambarwa zuwa yau, hukumomin Nijar ba su ce kala ba akai.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: