Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Rufe Iyakokin Kasashen ECOWAS Ka Iya Zama Barazana Ga Yaki Da Ta'addanci A Sahel


ECOWAS
ECOWAS

Masana sha’anin tsaro sun bayyana fargaba akan yiyuwar fuskantar koma baya a game da yaki da ta’addanci a yankin Sahel sakamakon matakin rufe iyakoki da kungiyar ECOWAS ta yi saboda saba alkawalin shirya zabe da gwamnatin rikon Mali ta yi.

Matakin mayar da kasar Mali saniyar ware a sahun kasashen yammacin Afrika sakamakon rashin nuna alamun shirya zaben da zai mayar da mulki a hannun farar hula abu ne da masana ke ganin ba zai hafar da da mai ido ba a fannin tsaro a yankin Sahel, ganin cewa rufe iyakokin kasar da makwaftanta ka iya zama wani shinge ga dakarun tsaro a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda kamar yadda mai fashin baki a fannin tsaro Alkassoum Abdourhaman ya bayyana.

Editan jaridar l’evenement jami’i a cibiyar nazari da bincike ta Nobert, Zango Moussa Aksar na cewa shugabanin kasashen CEDEAO ba su yi la’akari da abinda zai biyo baya ba kafin yanke hukunci akan kasar Mali.

Makwabciyar Mali wato kasar Aljeriya, wacce ba ta cikin kungiyar ECOWAS ta yi tayin sulhu ga bangarorin biyu, Masana sun yaba da wannan dattako na Aljeriya.

Sanannen abu ne cewa matsalar tsaron da ta addabi yankin Sahel shekara da shekaru wani abu ne da ya samo tushe daga yanayin da ake ciki a arewacin Kasar Mali, yankin da kungiyoyin ta’addanci suka mayar da shi matattara wanda kuma ke ba su damar tsallakawa Nijer da Burkina Faso yayin da sannu a hankali abin ya fara danganawa zuwa iyakokin jamhuriyar Benin da Cote d’ivoire.

Saurari Rahoton Sule Mumuni Barma.

Fargabar Masana Akan Takunkumin ECOWAS - 3'10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG